Ministan Lafiya Osagie Ehanire, ya ce kwararrun ‘yan Chana 15 din da ake ta cece-ku-ce a kan su, sun zo Najeriya ne domin taya gwamnati gig-gina cibiyoyin killace masu cutar Coronavirus.
Ya yi wannan bayani ranar Talata a lokacin da ya ke bayani a taron manema labarai na kullum da suke gudanarwa kan ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar Coronavirus.
‘Yan Chana sun zo tun a ranar 18 Ga Afrilu, kuma a lokacin ministan cewa ya yi sun zo ne domin su taimaka wajen “yaki da cutar Coronavirus.”
Ko a lokacin sai da Kungiyar Likitoci ta Kasa ta nuna rashin goyon bayan shigo da ‘yan Chana din.
Sai kuma aka rika surutai kwanan nan, ganin yadda aka daina ganin su, abin da har Minista Ehinare ya ce wa ‘yan jarida su daina damun kan su dangane da inda ‘yan Chana din suke.
Da aka matsa masa lamba, Ehinere kwanan baya ya yi subul-da-bakan cewa, “wadannan ‘yan Chana ba bakin Gwamnatin Tarayya ba ne, bakin kamfanin gine-gine ne na CCECC.
Ya ce wadannan likitoci daga China, kamfanin CCECC ne su ka dauki nauyin kawo su Najeriya.
“Amma kuma mu ne su ke yi wa ayyukan a wurare daban-daban. Domin taimaka mana wajen aikin dakile cutar Coronavirus.
“Su ne suka yi aikin cibiyar killace mutane ta Idu da kuma wani aikin NNPC da hadin guiwar THISDAY.
Ministan Cikin Gida ya ce sun kasa komawa kasar su ce saboda dakar hana-zirga-zirgar jirage a duniya.
Ya ce bizar iznin zaman kwanaki 30 aka ba su.
Kakudubar Yadda Najeriya Ta Tattago Likitoci Daga Chana
Likitocin Najeriya sun ki amincewa a ‘rakito’ likitocin Chana
Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ta yi fatali tare da nuna rashin amimcewa da shirin da Najeriya ke yi domin gayyato likitoci daga Chana su zo taya kasar yaki da cutar Coronavirus.
Gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar gayyato likitoci 18 daga Chana domin su yi abin da ta ce, “su taya likitocin Najeriya kokarin kashe mahaukacin kare, wato cutar Coronavirus.’
Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana bukatar gayyato likitocin a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sai dai kuma a wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Francis Faduliye ya fitar a ranar Lahadi da dare, ya ce bai ga dalilin da zai sa a gayyato su ba, domin idan an yi hakan, to tamkar watdi da na gida ne, a kamo abin da ke nesa.
Faduliye ya ce, “wannan abin takaici da kunya ne, kuma idan aka yi haka, to an tozarta likitocin Najeriya kenan, idan aka yi la’akari da gudummawar da su ke bayarwa a wannan mawuyacin hali ba yaki da cutar Coronavirus.”
‘Yan Najeriya da dama sun yi tir da sanarwar da Ehanire ya yi a ranar Juma’a, inda ya sanar da shirin da Gwamnatin Tarayya din ke yi ba gayyato likitoci 18 daga Chana, kasar da cutar Coronavirus ta fara yi mummunar illa.
Sai dai kuma Babban Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a na Kasa, Garba Abari, ya yi karin haske dangane da irin ayyukan da likitocin daga Chana za su yi idan sun zo Najeriya.
“Idan sun zo, za su sanar da Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa irin hanyoyi da dabarun da suka yi a Chana suka shawo kan Coronavirus a kasar su.”
“Wannan cuta ta game duk duniyar nan. Ta zama bala’i, wanda kowa ke kokarin shawo kan ganin an magance shi. Saboda haka mu ko ma daga ina za mu iya samun taimakon ganin an kawar da cutar, to mu na marhabin lale da wannan taimakon.”
Sai dai kuma NMA ta ce wannan ‘rakice-rakicen likitoci’, karya guyawun likitocin Najeriya da sauran jami’an kiwon lafiyar kasar nan zai yi. Idan aka dubi irin kokarin da suke yi a kokarin dakile cutar Coronavirus a kasar nan.
“Sannan kuma bai kamata ba a rika yin abin a lullube, domin doka ta nuna cewa sai da izni da kuma tuntuba da shawarar Kungiyar Likitoci da Likitocin Hakora ta Kasa tukunna.”
Discussion about this post