FITINAR ‘YAN BINDIGA: Katsinawa, Zamfarawa da Sakkwatawa 23,000 sun yi gudun hijira a Jamhuriyar Nijar cikin watan Afrilu

0

A yanzu haka akwai Katsinawa, Sakkwatawa da kuma Zamfarawa sama da 60,000 da ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar daga watan Afrilu na 2019 zuwa yau.

Adadin na su ya karu ne daga 40,000 zuwa 60,000, bayan da hare-haren ‘yan bindiga suka kara rarakar wasu mutane har 23,000 a cikin wata daya, wato kwanan nan a cikin watan Afrilu, 2020.

Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana haka a ranar Laraba, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Hedikwatar Hukumar a birnin Geneva.

Kakakin UNHCR, Bahar Baloch ne ya bayyana haka, tare da karin hasken cewa wadanda suka kara yin tururuwa a baya-bayan nan zuwa cikin Nijar, duk yawancin su na yankin Maradi ne, gari na biyun din girma a Jamhuriyar Nijar.

Ya ce duka 23,000 din sun fito ne daga jihohin Sokoto, Zamfara da kuma Katsina.

Ya ce hare-haren ‘yan bindigar ya kori wasu ‘yan kasar Nijar da ke makautaka da Najeriya daga gidajen su, har su 19,000.

Bahar ya kara da cewa yawancin ‘yan gudun hijirar mata ne da kakanan yara, wadanda suka yi cinkoso a Nijar.

Rahoton ya nuna matukar damuwa dangane da yadda aka samun yin yawan masu gudun hijirar haka, duk kuwa da cewa akwai dokar rufe kan-iyakoki da Najeriya ta kakaba.

Mahara na ci gaba da hai munanan hare-hare, musamman a jihar Katsina da Sokoto. Baya ga hare-haren da suke kaiwa a garuruwan kan-iyaka, ‘yan bindigar sun kuma hana mazauna kauyukan kananan hukumomin Dutsinma, Safana, Danmusa da Batsari zama lafiya.

Ko cikin Mayu sun kashe mutum 47 a wadannan kananan hukumomi. Sai dai kuma mazauna yankin sun ce a lissafin su, jimlar mutum 73 aka kashe a kauyuka daban-daban.

Cikin wannan makon ma sun kai hari yankin Batsari, har rahotanni daga wasu kafafen yada labarai suka rika nuno wani bidiyo, inda wata mata ke bada labarin yadda maharan ke wa mata fyade.

Binciken da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da har yau Gwamna Aminu Masari na Katsina bai kai ziyara a gaeuruwan da ‘yan bindiga suka kashe mutum 47 ba.

Share.

game da Author