Farashin danyen mai ya sake faduwa kasa warwas a kasuwannin duniya, biyo bayan sake bayyanar cutar Coronavirus karo na biyu.
Farashin ya fadi ne saboda fargabar cewa janye dokar hana fita ko hana zaben zirga-zirga da manya da kasashen duniya suka yi, zai sa cutar ta sake barkewa.
An samu rahoton sake barkewar annobar Coronavirus, a kasashen Koriya ta Kudu da China, kasashen da cutar ta fara yi wa mummunar barna daga farkon bayyanar cutar.
Stephen Brennoc na kamfanin hada-hadar mai na PVM ya kara jaddada dalilin da ya sa farashin danyen man ke yin faduwar-‘yan-bori daga ranar Talata din nan.
Dama kuma fitaccen masani kuma mai bincike a kan cututtuka masu yaduwa da ke Amerika, Anthony Fauci ya shaida wa Majalisar Dokokin Amurka cewa, akwai yiwuwar cutar ta sake yin mummunar illa a Amurka muddin aka soke dokar zaman gida dole, har jama’a suka rika fitowa su na gwamutsa sa juna.
Amurka ta yi asarar rayukan mutane sama da 80,000, wadanda cutar Coronavirus ta kashe.
Samfurin danyen mai na Brent LCOc1 ya sauka zuwa dala 29.42. Shi ma WTI ya sauka.
Faduwar darajar mai din a karo kusan na 5 cikin kwanaki 30, ya sa tilas za a rage yawan danyen mai da ake hakowa a duniya, har ganga milyan 8.1 a kowace rana.
Coronavirus ta ruguza tattalin arziki kasashe da dama, manya da kanana, musamman kasar Amurka, wacce ta fi kowace kasa karfin tattalin arziki, kuma ta fi kowace kasa amfani da kuma sarrafa danyen mai.
Matsalar farashin danyen mai dai ya sa Najeriya ta zabtare kasafin kudin ta. Ita ma kasar Saudiyya ta nunka harajin-jiki-magayi (VAT), har nunki uku. Sannan kuma ta janye tallafin kudin cefane na kowane wata da ta ke bai wa ‘yan kasar marasa galihu.