Duk mahaifin da ya tura dan sa almajirci, zai iya fuskantar hukuncin dauri da tara – El-Rufai

0

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi iyaye da su kasa kunnuwan su su saurare shi, cewa daga yanzu duk wanda aka samu ya tura dan sa Almajirci wani wura, zai iya fuskantar hukuncin dauri da tara.

El-Rufai ya yi wannan gargadi ga iyaye ne a wajen horas da Almajiran da gwamnatin Kaduna ta killace tana musu wankan tsafta domin zama mutane a cikin al’umma a Kaduna.

El-Rufai ya ziyarci makaranta Kurmin Mashi inda aka killace almajirai ‘yan asalin jihar da aka dawo dasu daga jihar Nasarawa su 200.

” Duk wani malamin da ya tattago yara da sunanan Almajirci zai fuskanci fushin gwamnati, za a daure shi kuma aci shi taran naira 100,000 zuwa 200,000 akan kowani yaro.

Ya kara da cewa duk almajiran da aka dawo dasu daga wasu jihohin kasar nan gwamnati za ta horas da su ta yi musu wankan tsafta domin zama mutane kuma ta saka su a makarantu kusa da iyayen su.

Ya ce kowa zai yi karatun Islama da boko amma kuma wannan karon a kusa da iyayen sa. ” Sanna kuma da zaran an kammala girgije wadannan yara sun yi ta-tas za mu mika su ga iyayen su hannu da hannu, kuma mu saka su a makaranta ga su ga iyayen su.

A nata jawabin kwamishin jin dadin al’umma Hafsat Baba, ta shaida cewa jihar Kaduna ta karbi almajirai akalla 900 daga jihohin Kano, Bauchi, Plateau da Nasarawa.

Sannan kuma gwamnat ta gode wa asusun UNICEF kan tallafa mata da take yi wajen tufatar da yaran da samar musu da abin da suke nema.

Share.

game da Author