Dole Sai Kasashen Afrika Sun Koyi Yadda Zasu Rayu Da Cutar Coronavirus Don Kaucewa Yunwa Da Karyewar Tattalin Arziki, Daga Mustapha Soron Dinki

0

A wannan yanayi na annobar coronavirus, wacce a zahiri take cinye abubuwa guda: Lafiya da tattalin arziki. A bangaren lafiya, cutar tana kama mutane, wasu suna warkewa, kadan daga cikin masu cutar suna mutuwa.

A babun tattalin arziki kuma, coronavirus ta samar da abinda ake kira “Lockdown” wanda yake cinye arzikin kasa kamar yadda wutar daji take cinye itace.

Tun bayan barkewar cutar a Wuhan na kasar Chana, wasu kasashen suka fara kulle iyakokin kasarsu kamar yadda cibiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayar da shawara. Dokar zaman gida dole ta zama rigakafin da duniya ta yadda da ita wajen dakile yaduwar cutar.

Hakan ba karamin illa yake yiwa tattalin arziki ba saboda babu maganar kasuwanci kowane iri ne. Dama kuma gashi tuntuni an rufe iyakokin kasa, babu maganar kasuwancin kasa da kasa.

Shin ko kasashen Afrika zasu iya rayuwa a cikin wannan yanayi na Lockdown? Gaskiya da wahala, saboda bambancin tattalin arziki. Misali, idan kasar Amerika, Ingila, Jamus, Spaniya, da Italiya sun jure, gaskiya kasashe Afrika ba zasu iya ba. Domin basu da karfi. Kaso 80 cikin dari (80%) na ‘yan Afrika suna rayuwa ne irin ta tsuntsu. A Cikin mutane 1.3 billion.

Misali, kasar Amurka ta bayar da tallafin rage radadin talauci ga ‘yan kasa fiye da na triliyan biyu (US$2.2 trillion) amma Amerikawa suna korafi sai an barsu sun fita neman abinci. Mutane irin na wadannan kasashen suna da karfin samu (income) fiye da na Afrika.

Bincike ya nuna cewa, kaso 2 ne cikin dari (2%) na mutane suke da 500,000 zuwa sama a asusunsu na banki. Kuma kaso 40% na mutanen Najeriya suna rayuwa ne a kasa da N380 a kowacce rana (NBS 2019).

Tun wuri gwara kasashen Afrika su samarwa da kansu mafita (African/local solutions to covid19), su daina saurin kwafo tsari irin na kasashen da suka cigaba. Su ma wahalar “lockdown” din suke sha.

Akwai bukatar kasashe irinsu Najeriya su sake tunani kamar yadda kasar Madagascar tayi. Ba daidai bane ace komai namu na aro ne. Mu daina dogara da tunanin wasu, bayan komai namu ba daya bane.

Kasar Chana, lokacin da cutar ta kama Wuhan, sai suka kulle iya nan da farko. Amma Shanghai da Beijing a bude saboda kada kasuwancin kasar ya tsaya.

Hakan ne yasa, ana cikin tsakiyar annobar amma Chana tana siyarwa da duniya kayan rigakafi irinsu takunkumin fuska da kayan gwajin cutar.

Najeriya, idan muna so su mu rayu da corona, zamu iya sakin mutane bayan mun inganta cibiyoyin lafiyar mu, samar da kayan gwaji (testing kits), kara wuraren kwantar da masu cutar (isolation centers) da kuma tirsasa mutane akan yin amfani da takunkumin fuska, abun wanke hannu da yin nesa-nesa da juna.

Allah ya karemu.

Share.

game da Author