Yanzu haka kudirin kokarin kafa dokar dakile yaduwar ciwon ‘sikila’ ya kusa tabbata, domin har Majalisa ta yi masa karatu na biyu.
Daga cikin kudirin, akwai dokar da ake son kafawa wadda za ta haramta aure tsakanin mai nau’in jinin sa ke ‘AS’ da wadda nau’in jinin ta ke ‘SS’.
Wannan doka za ta hana duk mai nau’in jini AS da SS ya auri wani mai ciwon ‘sikila’ kuma.
Wannan Kudiri wanda Sanata Sam Egwu ya gabatar da shi, ya na so a kafa dokar ce domin a takaita yawaitar mutane da dakile yaduwar cutar a cikin jama’a tare da dakatar da rayuwar kuncin da masu fama da ciwon ke yi a tsawon rayuwar su.
Masana sun hakkake cewa akwai dubban jama’a a kasar nan, wadanda ke fama da wannan ciwo ba dare ba rana.
Su na ganin cewa ciwon ya na yaduwa ne saboda yawaitar auratayya tsakanin ma’auratan da jinin su bai dace da na juna ba.
Wannan cuta wadda kusan gadon ta ake yi, kusan akwai ta a jikin kashi 5 bisa 100 na al’ummar duniya. Sai dai kuma ana hasashe da kirdadon cewa ta fi muni a Afrika.
An kiyasta cewa akwai yara 300,000 da ke haihuwa da wannan cutar a duniya, to kashi 75% bisa 100% na wadannan jarirai duk a yankunan Saharar Afrika suke.
Cibiyar Dakile Cututtuka ta Amerika ta shaida cewa kashi 66% bisa 100% na kashi 75% din can, duk a Najeriya suke.
Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa kashi 24 bisa 100 na daukacin ‘,yan Najeriya na dauke da birbishin wannan cuta, sannan ka a duk jarirai 1,000 da aka haifa a Najeriya, akan samu 20 masu dauke da cutar.
Da ya ke kara bayani a kan kudirin dokar, Sanata Egwu ya ce wannan cuta ta na ci gaba da yi wa jama’a illa sosai tare da daukar rayukan su, amma kuma ba a san ta ba sosai kuma babu wani hobbasa da ake yi domin shawo kan ta.
Da ya ke bada gudummawar goyon baya, Sanata Biodun Olujimi daga jihar Ekiti, ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da a tashi domin a yi hobbasa a shawo kan cutar. Kuma ya ce a tallafa wa cibiyoyin binciken janyoyin shawo kan cutar.
Shi kuwa Sanata Chukwuka Utazi, bada labari ya yi irin yadda ya shafe shekaru biyar ya na fama da cutar, ko fita waje ba ya iya yi.
Daga nan sai ya ce ya san cutar kuma ya sha fama da ita tsawon lokaci. Don haka ya zama wajibi a daina aure tsakanin masu cutar domin a hana yaduwar ta.
“Mu a nan Afrika mu na da matsalar haife-haife barkatai. Sannan kuma aure ake yi ba na soyayya ba. Kamata ya yi a rika awon jini domin tabbatar da cutar.”
Ya kara da cewa, “bai ma kamata ba a ce wai a bari har sai an tashi aure sannan a yi gwajin jinin ma’auratan ba”.