Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta fitar da jerin rukunin wadanda dokar hana tafiye-tafiye da zirga-zirga ba za ta hau kan su ba.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Kasa, Frank Mba ya fitar, a madadin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, ta ce wadanda dokar ba ta hau kan su ba, su ne likitoci, jami’an kiwon lafiya, direbobin motocin daukar marasa lafiya, jami’an kashe gobara da ‘yan jarida.
Wannan sanarwa ta biyo bayan fusatar da Kungiyar Likitocin ta Kasa, Reshen Jihar Lagos ta yi, ta shiga yajin aikin zaman gida.
Likitocin sun nuna damuwa ne a bisa tare su da jami’an ‘yan sanda ke yi idan sun fita aiki har ana kama su.
Wannan ya sa sun shiga yajin aikin zama gida, tun daga ranar Laraba, karfe 6 na yamma.
Sanarwar da Sufero Janar ya fitar, ta umarci dukkan Mataimakan Sufeto Janar na Shiyyoyi (AIG) da Kwamishinonin ‘Yan Sanda su tabbatar jami’an su ba su rika kama wadannan rukunin ma’aikatan ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda likitocin Lagos suka buga sanarwar tafiya yajin aiki, tare da umartar Gwamnatin Jiha da Kwamishiman ‘Yan Sanda su ba su tabbataci a rubuce cewa ‘yan sanda ba za su kara tare su su na tozarta su ba.
Sun kuma Nami su buga sanarwar a kafafen soshiyal midiya da jaridu kowa ya gani domin a tabbatar.
Ba likitoci da ‘yan jarida kadai ba, jama’a su na ci gaba da kokawa dangane da yadda jami’an tsaro ke gallaza wa mutane da sunan tirsasa bin dokar zaman gida da ta hana tafiye-tafiye.
Da yawa sun rasa rayukan su sanadiyyar bindige su da jami’an tsaro suka yi, a cikin wadannan Watanni uku.
Tuni dai likitocin na Jihar Lagos sun koma bakin aikin su, bayan da aka sasanta da su.
Discussion about this post