DOKAR KANO: Buhari ya kulla, Ganduje ya warware, ko kuwa Ganduje ne ya Kulla Buhari ya warware – Daga Gambo Dan Lawal

0

Tun bayan sanar da karin makonni biyu na kulle da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Saka a jihar Kano, da kuma sanar da bude masallatai domin yin sallar juma’a da kuma yin sallar Idi da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya amince ayi mutane suka yi to tofa albarkacin bakinsu kan da haka.

Ashe shugaban kasa bai isa ya saka doka da ya shafi jiha abi dole ba? Wannan shine tambayar da mutane suka rika yi a shafukan sada zumunta a yanar gizo.

Idan ba a manta ba, a farko dai shugaba Buhari ya saka dokar zaman kulle a jihohin Legas, Ogun da babban birnin tarayya, Abuja. Shugaba Buhari ya kara wasu makonni biyu, haka kuma jama’a suka bi dokar a wadannan jihohi da babban birnin tarayya.

Ranar litinin, Buhari ya saka hannu a dokar a kara wa jihar Kano makonni biyu na zaman gida dole, wato na kulle.

Jim kadan bayan bayyana wannan doka sai gwamnan Kano Ganduje ya sanar cewa ya janye dokar hana sallar Juma’a da aka saka a jihar domin dakile yaduwar cutar Korona sannan kuma ya amince kowa ya fito a cakudu a tafi sallar idi.

Wannan mataki da Ganduje ya dauka ya sa ana ta maganganu game da ko waye ke da iko a kan jiha, shugaban Kasa ne ko gwamna?

Wasu na ganin koda Ganduje zai yanke wannan hukunci bayan ganawa da malamai da yayi a jihar, ya tattauna da gwamnatin tarayya tunda ta saka wannan doka kafin ya gana da malamai da limamen jihar ko kuwa Buhari ne ya kamata ya saurara tukuna kafin ya yanke hukuncin saka hannu a wannan doka da ya saka na kara wa Kano makonni biyu na kulle.

Wasu na ganin ashe dai yin biyayya ga doka daga Abuja ba dole bane tunda gwamna ma yana da ikon ya saka dokar sa ko kuma ya janye ko da ko shugaban kasa ya sa dokar a kan jihar sa.

Babban tambayar anan dai kamar yadda masu karatu suke ta tsokaci akai da tambaya shine, shin wanene ya kulla kuma wanne ya ya warware?

Share.

game da Author