Dokar hana ibada a masallatai da coci-coci ta raba kawunan ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

0

Dokar da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa, wadda ta hana gudanar da sallar Juma’a a masallatai da kuma ibada a coci-coci, ta raba kawunan ‘yan majalisar jihar.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa dokar hana zirga-zirga, ibada a masallatai da coci-coci, tare da hana taron jama’a yin cincirindon jama’a.

An kuma rufe kasuwanni. An daina sallar Juma’a da zuwa coci a ranakun Lahadi.

An kuma hana gudanar da tafsir da aka saba yi ana kunna lasifika ana yi a masallatai, domin kauce wa cinkoson jama’a.

Sai dai kuma wannan bai sa jama’a sun daina halartar salloli biyar a kullum ba, duk kuwa da cewa an hana.

Sai dai kuma tayar da batun da aka yi ranar Laraba a Majalisar Dokokin jihar, ya raba kan ‘yan majalisar, yayin da mafi yawan su ke neman gwamnati ta janye dokar, a bar kowa ya yi ibadar sa a masallatai da coci-coci.

Cikin wadanda ke neman a dage dokar, akwai Honorabul Tijjani Aliyu mai wakilta Kananan Hukumomin Azare da Madangale, Yusuf Dadiye, na Ganjuwa, Dan’umma Bello na Giade da Jamilu Danlami na Karamar Hukumar Bauchi ta Tsakiya.

Bello ya ce bai ga dalilin da a hana zuwa yin ibada ba. Don haka inji shi, a bar kowa ya yi idabar sa kawai.

Ya ce jama’ar da ya ke wakilta su na ta kiran sa au na damun sa a kan don me za a hana su fita yi ibada.

Tijjani Aliyu na ganin cewa an tsaurara dokar, domin har Giade da Zaki inda cutar ba ta yi barna ba a saka dokar hana ibada a masallatai da coci-coci sai da ta shafe su.

Jihar Bauchi ta samu mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar, bayan Gwamna Bala Mohammed ya bayyana kamuwa da cutar, cikin watan Maris.

Tuni Bala ya warke, amma cutar ta ci gaba da bulla wasu yankunan jihar.

Share.

game da Author