Matsalolin tabarbarewar tattalin arziki na neman zame wa ‘yan Najeriya gaba damisa baya siyaki, yayin da aka wayi gari darajar dalar Amurka daya ta kai daidai da naira har N445.
Duk wa wannan tsadar da dala ta yi, wanda ya kara janyo ta kara gurgunta naira, ta rage mata daraja a kasuwar hada-hada, hakan bai sa dalar ta wadata ba.
A wannan mummunan hali da ake ciki na annobar Coronavirus, kasuwar hada-hadar komai ta tsaya cak, yadda ba a tasarifin manyan kudade a bankuna, ko sabat-ta-juyat-tar cinikayyar manyan kadarori musamman a bankuna.
“Wannan al’amari ya yi muni ne, saboda Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin rufe filayen jiragen samar kasar nan, sakamakon cutar Coronavirus. ” Haka Shugaban Kungiyar ‘Yan Canji, Aminu Gwadabe ya shaida wa manema labarai.
Ya kara da cewa wani dalilin da ya sa dala ta kara tsada a kasuwa kuma shi ne, saboda Babban Bankin Tarayya ya dakatar da sayar wa ‘yan kasuwar-tsaye dala kai-tsaye, ya ce har sai an bude filayen giragen sama tukunna.
Gwadabe ya ce wannan ne dalilin da ya sa darajar naira ta kara karyewa, ita kuma dala ta kara tashi daga N425 zuwa Naira 445.
Sai dai kuma alkawarin da Gwamnan CBN ya yi wa masu zuba jari daga kasashen waje cewa ba za a bari dala ta kara yin tashin-gwauron-zabo ba, ya sa tun da dalar ta kai naira 445 har yau ba ta kara yin gaba ba.
PREMIUM TIMES ta fahimci cewa bankuna sun fara sayar da dala ga masu biyan kudaden makarantar ‘ya’yan su a kasar waje, sai kuma ga kananan ‘yan kasuwa.