Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, wato African Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina ya kare kan sa daga zargin harkallar da wasu ‘yan sababin ma’aikatan bankin suka yi masa, ta hanyar aika rubutaccen korafi a kan sa.
Wadanda suka aika da korafin dai har yau ba a san ko su wane ba. Sun aika da korafin a ranar 19 Ga Janaidu, kamar yadda Premium Times ta buga labarin a ranar Talata.
Ranar 7 Ga Fabrairu Kwamitin Ladabtarwa ya aika wa Adesina kwafen zarge-zargen da ake yi masa, sannan aka nemi ya yi bayani.
Ranar 10 Ga Fabrairu d 10 Ga Maris, Adesina ya aika da amsa ta hannun lauyan sa, amma ko karanta wasikar kwamitin bai yi ba. Sun ce ai bai sanar da su cewa lauya zai maida amsa a madadin sa ba.
Ranar 8 Ga Afrilu, Adesina ya maida amsa, inda ya bi dukkan zarge-zargen da ake yi masa daya-bayan-daya, ya rika kare kan sa.
Harkalla: Yadda Akinwumi Adesina Ya Kare Kan Sa
1. Ya ce zarge-zargen gaba dayan su ba korafin ya aikata wani laifi ba ne, wasu algungumai ne ke kokarin hana shi ci gaba da shugabancin bankin.
2. Batun daukar Chinelo Anahu-Amuzo aikin: Adesina ya ce bai yi gaban kan sa wajen daukar ta aiki ba. Talla aka buga duk duniya kuma an gani cewa za a dauki masu mukamin da aka nada ta. Hasali ma ya ce kamfanin buga tallace-tallace na Russell Reynolds da ke Birtaniya ne ya tallata gurbin da Chinelo ta cike, bayan an tabbatar da cewa ta cancanta.
3. Zargin daukar surikin sa Martin Fregene aiki: Akinwumi Adesina ya ce Martin ba surukin sa ba ne, ko da wasa ko da gaske. Ya ce kuma ba shi ya dauke shi aiki ba, Jennifer Black ce ta dauke shi aiki.
4. Zargin harkalla a kwangilar ayyukan TAAT: Adesina ya ce ko kadan bai aikata wani laifi ba. Amma ya san akwai inda aka yi kuskure, wanda ya ce an kafa kwamitin binciken da bai bayar da rahoton sa ba tukunna.
5. Zargin daukar Maria Mulundi aiki: Ya ce tabbas ya san ta kuma ta yi aiki da shi a baya. Ta na daga cikin ‘yan fadar sa da ya kafa wadanda tun farkon nada shi ya nemi aiki tare da sun domin ya yi nasara.
Sannan ya ce ka’idar aiki ta nai wa kowane shugaban bankin AfDB ya dauki shugaban ma’aikatan sa wanda ya ke son dauka. Haka mashawar ta ma, sai wanda ya ga damar dauka.
6. Zargin daukar abokin sa Victor Oladokun aikin jami’in tuntuba: Adesina ya ce don ya san Victor tun su na firamars, doka ba ta hana ya dauke shi ba, tunda ya cancanta.
8. Zargin daukar Kapil Kapoor aiki: Adesina ya bayar da dalilan irin aikin da ya ke yi, wadanda suka jibinci wasu ayyukan da ya yi wa bankin. Sannan kuma ya ce Kapoor ya yi ritaya tun cikin watan Agusta, 2019.
9. Zargin daure gindin daukar Emmanuel Ezinwa aiki: Adesina ya ce bai san shi ba, kuma bai taba ganin sa ba.
Ya ce da farko ya na aiki ne a matsayin gwaji, kafin ya zama ma’aikacin dindindin. An zarge shi da laifin latsa wata mata har aka kafa kwamitin ladabtarwa, zai ba a same shi da laifin komai ba.
10. Zargin fifita ‘yan Najeriya: Ya ce duk wani abu da ya aikata ba sabon abu ba ne, haka tsarin bankin ya ke tun kafin ya hau shuhabanci. Kuma idan ma ya sauka, haka wanda ya hau zai yi, saboda muhimmancin Najeriya a bankin.
11. Zargin biyan kudade aka ba shi Lambobin Yabo: Adesina ya ce bai bayar da ko sisi ba. Lambar girmamawa kuma shi aka ba, amma ai bankin AfDB ya kara samun martaba da daukaka.
Dala 250,000 da dala 500,000 kuma ya bayar ne ga Asusun Gidauniyar Tara Abincin Koyar Yunwa ta Duniya.
Ya ce ‘yan rakiya, ‘yan rawa da makada daga Najeriya da sauran ‘yan a bi Yerima a sha kida, duk WFPF ce ta dauki nauyin su.
Sauran Zarge-zarge: Ya ce duk ba gaskiya ba ne, bai aikata laifi ba.
Zargin kutsa kai cikin manyan ‘yan siyasa: Ya ce karya ce ake yi masa bai ba shugabannin Afrika ta Yamma su 16 cin-hancin ko sisi ba. An kirkiri zargin ne kawai don a bata masa suna.