DALLA-DALLA: Yadda aka fallasa harkallar Adesina, Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (AfDB)

0

Gwamnatin Amurka ta nemi a sake sabon binciken zargin harkallar da aka yi wa Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina.

Wannan kira ya biyo bayan da Kwamitin Ladabtarwa na AfDB ya wanke Akinwumi Adesina daga dukkan zarge-zargen da wani dan sababin magulmaci a cikin bankin ya yi masa.

Magulmacin ya cunna wa Akinwumi hayakin da ya sa idanun sa yin ja-wur, har sai da ta kai shi ga rubuta raddin neman mafita mai shafuka 260.

Ganin cewa Akinwumi Adesina ba shi da wani abokin takarar neman shugabancin bankin nan da wasu shekaru biyar, hakan ta sa a Amurka an nemi wani kamfanin bincike na musamman, wanda babu ma’aikacin AfDB a cikin su ko daya.

Amurka wadda ita ma mamba ce a bankin tun cikin 1983, ta rubuta wa Shugaban Hukumar Daraktocin AfDB, Niale Kaba, a ranar 22 Ga Mayu, 2020 cewa ba ta gamsu da sakamakon binciken-cikin-gida da bankin ya yi ya wanke Shugaban su, Adesina ba.

“Ba mu gamsu da gagarta da gaskiyar dukkan ‘yan Kwamitin Bincike ba. Saboda haka ka sake kafa wani kwamifin bincike mai zaman kan sa kawai, wanda duniya ta yarda kuma ta gamsu da sahihanciin sa, ba wasu daga cikin mahukuntan bankin ba.” Haka Shugaban Baitulmalin Amurka, Steven Machin ya rubuta, ya aika wa Niale Kaba.

“Tsoron mu shi ne, irin yadda aka gaggauta wanke wanda ake zargi daga laifi, ba tare da zurfafa bincike ba, hakan zai iya zubar da duk wata kima da kwarjinin da AfDB ke da shi, har martaba da ingancin sa su dusashe baki daya.”

Dalla-dalla: Zarge-zargen Harkalla Da Cuwa-cuwar Da Aka Yi Wa Adesina

Ranar 26 Ga Afrilu, Kwamitin Bincike a karkashin wani dan kasar Japan mai suna Takuji Yano, ya wanke Adesina daga dukkan zarge-zargen da wasu magulmatan ma’aikatan bankin su ka yi masa. Sun rubuta takardar zargin tun a ranar 19 ga Janairu.

Yayin da kwamiti ya zargi masu korafi da kasa bayar da gamsassun bayanai, tare da kin amsa gayyatar sanarwa cewa wadanda suka yi korafin su bayyana a gaban kwamiti.

Su kuma masu korafi sun ce su na tsoron bayyana kan su, tunda a asirce suka aika da korafin, ba tare da bayyana kan su ba.

Sannan kuma sun yi zargin cewa an yi kokarin binne korafin na su, domin sai da aka shafe makonni shida babu abin da aka yi a kai.

Suka ce sun ki bayyana kan su ne, domin da farko maimakon a yi bincike, sai aka yi ta kokarin gano ko su wane ne suka rubuta takardar korafe-korafen. Sai da suka watsa takardar ta su a wurare da dama, sannan bankin ya ya fara nade tabarmar-kunya, ya kafa kwamitin bincike.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya Adesina murnar wanke shi da kwamitin ya yi. Ita kuma Amurka ta ce a dai sake bincike.

Zarge-zarge:

Zarge-zargen da aka yi wa Adesina sun kai 20, wadanda suka hada da: Karya ka’idoji, fifita wasu akan wasu, daukar wasu aiki ba bisa ka’ida ba, azurta kan sa, kawo cikas ga nagartaccen aiki, ko kuma hana-ruwa-gudu, daukar hukuncin gaban-kan sa, ya watsar da abin da daraktoci suka aiwatar, bangaranci da kabilanci da kuma amfani da kudin bankin ya na balle-bushasha a duniya.

1. Ya nada Chinelo Amazu babban mukami, bayan Shugaba Buhari ya kore ta daga shugabancin PenCom. An kore ta 2017, shi kuma ya nada ta cikin 2018.

2. Ya nada surikin sa Martin Fregene mukamin darakta. Fregene kuma ya yi masa PA a lokacin da Adesina ke Ministan Harkokin Noma a Najeriya. An nada Fregene ba tare da an tallata mukamin na sa ga wadanda suka cancanta ba.

3. Ya nada wata kawar sa Maria Malundi ‘yar kasar Kenya wani mukamin jami’ar tuntuba. Hakan ya sa wata Daraktan Stella haushin yin murabus, saboda ta ga ya na biyan kawar sa makudan kudaden da suka wuce misali.

4. Fifita wani tsohon abokin sa mai suna Victor Olasokun. Abokin sa ne tun su na yara kanana. Ya ba shi wani aikin da ya ke biyan sa dala 320,000 tun a cikin 2017. Kuma kudin bankin ake kwasa ake biyan sa.

5. Ya dauki wani mai suna Kapil Kapoor aiki. Kapoor tsohon Daraktan AfDB ne, mai kula da kasashen Kudancin Afrika.

Amma ya yi ritaya, sai Adesina ya dauke shi aikin kwantiragi, ya na biyan sa dala 26,000 wata.

Masu korafin sun ce an maida Kapoor Ofishin AfDB da ke Pretoria, Afrika ta Kudu, inda ya ke nuna isa a can, duk kuwa da cewa akwai Mataimakin darakta a can mai kula da ofishin.

6. Kawar sa Maria Mulundi da ya yi wa karin mukami zuwa ofishin Shiyyar Afrika ta Kudu, an yi zargin ya maida ita can ne domin ta rika kula da matar sa wadda ke zaman jiyya na tsawon lokaci a Afrika ta Kudu.

7. Adesina ya tilasta Daraktar Daukar Ma’aikata, ta dauki wani dan Najeriya aiki. An dauki Emmanuel Ezinwa ma’aikacin dindindin, bayan ya ci mutuncin wani a lokacin da ya ke zaman aikin gwaji na wucin-gadi. An ce bai cancanta a dauke shi ba, amma Adesina ya ce lallai a dauke shi.

Hakan ya fusata Daraktar, ta ajiye aiki watanni shida da kama aiki a AfDB.

8. Yin amfani da karfin siyasa ya na basa tallafi da lamunin milyoyin daloli ga cibiyoyi da hukumomi. Sun bayyana yadda ya sa aka bai wa wasu cibiyoyin da ya taba yin aiki dala milyan 40.

9. Ya narkar da kudin bankin har dala 250,000 tukuicin wata lambar girmamawa da wata cibiya ta ba shi a Amurka. Kuma ya kashe dala 500,000 daga kudin bankin wajen dabdalar karbar wata kyauta a Seoul, Korea ta Kudu.

Adesina dai ya kare kan sa cikin wani raddi mai shafuka 260. Ya ce magulmatan duk ‘yan kamasho ne, wasu ne suka biya su kudi don su bata masa suna kawai.

Sai dai Amurka ba ta yarda da wankiyar da kwamiti ya yi masa ba.

Share.

game da Author