Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tsawaita dokar Zaman Gida Dole da mako daya.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta saka dokar hana walwala da zaman gida dole na makonni biyu a jihar Kano domin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
Kwamishinan Yada labarai, Muhammed Garba ya bayyana cewa gwamnati ta kara mako daya ne domin yin biyayya ga shawarwarin ma’aikatan kiwon lafiya na rage yawan gwamatsuwar mutane a jihar wadda shine hanya mafi girma da ake yada cutar.
Gwamnati tace tana ci gaba da aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
Bisa ga sanarwar, gwamnati ta yi kira ga mutane da su yi hakuri su bi doka da kiyaye hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.
Mutum 666 suka kamu da cutar Korona a jihar Kano, 63 sun warke, 32 sun mutu.