Dalilin da ya sa Ganduje ya janye dokar hana sallar Juma’a ya kuma amince a yi sallar Idi a Kano

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya janye dokar hana sallar juma’a sannan Kuma ya amince a yi sallar idin karamar Sallah idan an ga wata ranar Asabar ko Lahadi.

Kakakin gwamnatin jihar Kano, Salihu Tanko ya shaida cewa gwamna Ganduje ya gana da manyan malamai 30 a jihar na sama da awa biyu. A karshen ganawar gwamnatin jihar ta amince amince a janye dokar hana sallar juma’a a jihar sannan kuma idan Allah ya kai mu ranar Asabar ko Lahadi za a yi sallar idi.

” Gwamnati ta amince al’umma su halarci sallar Idi ranar sallah a duk fadin jihar. Sai dai ya ce a bi ka’idojin da gwamnati ta saka domin kiyaye kamuwa da cutar Korona.

” An umarci Malaman Masallatan Juma’a da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka takunkumin fuska ya kuma wanke hannaye da saka sanadarin tsaftace hannaye sannan a raba sahu kuma kuma a saka jami’an hizba su tabbata an bi wadannan dokoki.

Idan ba a manta shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar Zaman Gida Dole a jihar Kano da mako biyu. Wannan amincewa ta fito daga shugaban kwamitin Dakile yaduwar cutar Korona, Boss Mustapha ranar Litini.

Dama kuma gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar da mako daya.

A wannan taron manema labarai shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.

Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.

” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.

” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.

CORONAVIRUS: Ku saurari sabbin matakai daga Buhari ranar Litini – Boss Mustapha

Wannan Sanarwa ya shafi jihar Kano da a makonni biyu da suka gabata shugaba Buhari ya saka dokar ‘Zaman Gida Dole’ a dalilin barkewar annobar korona a jihar.

Wannan doka dai ya nuna cewa jihohi da dama ba za su samu damar zuwa sallar Idi ba idan allah ya kai mu an kammala azumin watan Ramadan.

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 338 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Lahadi.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Lahadi, Jihar Legas ta samu karin mutum 177, 64-Kano, 21-FCT, 16-Rivers, 14-Plateau, 11-Oyo, 9-Katsina
4-Jigawa, 4-Kaduna, 3-Abia, 3-Bauchi, 3-Borno, 2-Gombe, 2-Akwa Ibom, 2-Delta, 1-Ondo, 1-Kebbi, 1-Sokoto.

Yanzu mutum 5959 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1594 sun warke, 182 sun mutu.

Share.

game da Author