Dalilan da ke sa Korona ke wa attajirai da manyan mutane kisan-farat-daya -Ministan Lafiya

0

Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana dalilan da ya sa ake ganin cutar Coronavirus ke kashe manyan kasar nan, kisan da wasu ke tunani kamar kisan farat-daya-ne.

Da ya ke bayani a taron manema labarai na kowace rana, dangane da ci gaba da a ke samu a kokarin dakile cutar Coronavirus, Ehanire ya ce yawancin masu hali idan ciwon ya kwantar da su, sai su gwammace su rika yin magani a gida.

“Sai bayan ciwo ya ci karfin jiki sannan za a garzaya asibiti. Da an auna kuma sai a ga ashe Coronavirus ce.

“Ba wai sai masu kwantaccen ciwo ne cutar ta fi saurin kashewa ba. Wasu rashin lafiya ce za ta same su, amma ganin su na da hali, sai su yi kokarin yin magani a gida.”

Mutum na farko da Coronavirus ta fara kashewa a Najeriya, Suleiman Achimugu, tsohon shugaban kamfanin PPMC ne da ke karkashin NNPC.

An tabbatar da cewa ya je niyya ce kasashen waje, ya dawo da Coronavirus a Najeriya.

Shi ma Abba Kyari, Coronavirus ce ajalin sa. Ya mutu ya na kan mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, wanda ake kallon cewa ya fi kowa kusanci da Buhari.

Ya zuwa ranar Laraba, Coronavirus ta kashe mutum 192 a Najeriya, kuma mutum 6,401 ne su ka kamu.

A na sa jawabin Shugaban Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa (NCDC), Chikwe Ihekweazu, ya ce ba wai yawan tulin alkaluman masu kamuwa da cuta ko karancin su ne ke sa gwamnatin tarayya tura wa jiha kudi domin ta yaki Coronavirus ba.

“Tura wa jiha kudi don yaki da Coronavirus ba shi da akala da yawan masu cutar a jihar.” Inji Ihekweazu.

An dai yi zargin cewa akwai jihohin da ke yin aringizon yawan alkaluman da suka kamu, domin samun kudi daga gwamnatin tarayya.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sha tsangwama a lokacin da ya roki naira bilyan 15 daga gwamnatin tarayya domin dakile Coronavirus a jihar Kano.

Share.

game da Author