Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shi da kan sa zai yi aikin sintiri a iyakan Kaduna da Kano ranar Sallah kora maida duk wanda yake so ya shigo Kaduna daga Kano.
El-Rufai ya fadi haka a hira da yayi da tashoshin radiyon Kaduna kaitsaye ranar Talata.
” Na sha wahala matuka a lokacin da na kwanta bani da lafiya. Cutar Korona ba cutar da za a yi mata wasa bane.
” Sannan kuma mun samu gagarimin matsaloli da jami’an tsaron ‘yan sanda dake tattare iyakokin Kaduna saboda karbar toshiyar baki daga matafiya da suke yi suna barin su na shiga jihar mu. Jami’an tsaro sun ci amanar mu duk da dokar da shugaban kasa ya saka. Suna karya doka da kansu.
Baza mu janye dokar Zaman Gida Dole ba
Gwamna El-Rufai ya kara da cewa har yanzu babu lokacin janye dokar zaman gida dole saboda haka kada mutane su sa ran za a bude jihar Kaduna nan kusa.
” Muna da tsari na yadda za a janye dokar zaman gida dole a Kaduna. Ba za muyi gaggawar janye doka ba. Cikin shirin da muka yi ya hada da gina wuraren killace wadanda suka kamu, da kuma wuraren yin gwaji. Sannan kuma mun sa a dinka mana takunkuma fuska miliyan biyu. Zamu raba wa mutane a kasuwanni da sauran wuraren da jama’a suke cinkoso.
Bayan haka gwamna El-Rufai ya yi karin bayani game da cewa da ake yi wai an kirkiro cutar a Kaduna ne domin gwamnatin Tarayya ta ba mu kudi kamar yadda ta ba gwamnatin Legas.
” Tun da muka fara yaki da wannan cuta ba a bamu ko sisi daga Abuja ba. Da kudin mu muke aiki. Saboda haka wannan magana ce ta ‘yan adawa ne.
Mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe, Sakataren gwamnatin Kaduna, Samuel Aruwan da Hafiz Bello duk sun yi karin haske game da ayyukan da gwamnatin jihar ke yi don kauce wa yaduwar cutar a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Kaduna ya kara da cewa a cikin wannan mako za a rabawa wa talakawar Kaduna abincin tallafi.
” Za a rabawa talakawa abincin tallafi kafin sallah.”
Discussion about this post