Cutar tsutsar Timatir ya barnata gonakin Timatir a Kano

0

Shugaban Kungiyar manoman tumatir na jihar Kana (TOGAN), Sani Danladi ya bayyana cewa cutar tsutsan tumatir wanda aka fi sani da ‘Tomato Ebola’ ya sake bullowar a jihar inda yake barnata timatir a gonakin manoma.

A tattaunawa da yayi da PREMIUM TIMES, Danladi ya ce cutar tana barnata tomatir da ba za a iya amfani da tomatirin ba.

Idan ba a manta ba a shekarar 2016 an yi fama da irin wannan cuta da ya barnata gonaki, kuma Tomatirin yayi bakin tsada matuka.

Manoman tumatir sun yi asaran mai dimbin yawa a lokacin kamar yadda hakan ke neman doso kai yanzu.

A Wannan shekaru manoman tumatir sun yi asarar akalla Naira biliyan 2.

Manoman tumatir a Kano, Jigawa, Katsina, Gombe, Filato da babban birnin tarayya Abuja na cikin wadanda suka yi asara a wannan shekaru.

“Duk shekara idan aka yi zafi a jihar Kano manoma na fadawa cikin irin wannan matsala.

“Mun yi kokarin shuka wani sabon irin tumatir domin gujewa wa matsalar lokacin zafi amma Allah bai sa an yi nasara ba.

Sannan kuma baya ga matsalar da suka fada a dalilin annobar Coronavirus Danladi ya ce manoman Tomatir sun yi asara matuka saboda matsalolin rashin karakaina da fadi tashi na ayyukan gona, sai gashi kuma yanzu da suka dan samu dama cutar tsutsan tomatir ya danno.

“Mun shuka irin timatir a tsarin Anchors Borrowers Programme sai dai kashi 10 bisa 100 ne kawai suka toho a gonakin mu, duk sauran sun mutu.

“Da hekta 2500 da muke shuka sun yi kyau da farashin tumatir ya sauka raba-raba.

“Manoman tumatir dake shirin Anchors Borrowers Programme sun yi asarar gaske a dalilin matsaloli da suka yi ta fama da su. Yanzu muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki cikin gaggawa.

Share.

game da Author