Alkaluman sakamakon binciken da Jami’ar John Hopkins ta gabatar ranar Juma’a ya nuna cewa mutum sama da 259,000 suka mutu a sanadiyyar fama da suka yi da cutar Coronavirus a duniya.
A bisa wadannan alkaluma, hakan ya nuna cewa duniya ta samu karin mutum 100,000 da suka mutu daga ranar 17 ga watan Afrilu zuwa yanzu.
Rahotan ya nuna cewa kasar Amurka ke kan gaba wajen yawan wadanda suka mutu a dalilin cutar a duniya.
Kasar Amurka na da mutum 68,689, Italiya na da mutum 29,079, Britaniya na da mutum 28,809 sannan Faransa mutum 25,204 da suka mutu.
Kasar Chana kuwa wacce a kasar ta ne aka yi kyankyasar cutar ta rasa mutum 4,637 ne. Sai dai wasu masana na ganin akwai lauje a nadi bisa ga wadannan alkalumma da kasar ta fidda na yawan wadanda suka mutu a sanadiyya cutar.
Binciken ya kuma gano cewa mutum sama da 3,578,000 ne suka kamu a duniya. Duk da haka kasar Amurka ne ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar a duniya.
Har yanzu duniya na ci gaba da fama da annobar coronavirus, sai dai a hankali ana rage tsauraran matakan da aka saka a domin kauce wa yaduwar cutar.
A Najeriya ma hakan bai sauya zani, domin gwamnatin tarayya ta sassauta dokar hana walwala da ta kakaba a jihohin Legas, Ogun da babban birnin tarayya.