Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 206 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.
A alkaluman da NCDC ta fitar ranar Juma’a, Jihar Kano ta samu karin mutum 92, 36-FCT, 30-Lagos, 16-Gombe, 10-Bauchi, 8-Delta, 6-Oyo, 5-Zamfara, 5-Sokoto, 4-Ondo, 4-Nasarawa, 3-Kwara, 3-Edo, 3-Ekiti, 3-Borno, 3-Yobe, 2-Adamawa, 1-Niger, 1-Imo, 1-Ebonyi, 1-Rivers
1-Enugu.
Yanzu mutum 2170 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 351 sun warke, 68 sun mutu.
Abu fa sai gaba-gab yake yi yanzu. Maimakon baya sai gaba ake samu. Baya ga yaduwa da cutar tayi zuwa kusan duka jihohin kasar a kullum karin ywan wadanda suka kamu ake samu maimakon raguwa.
Jihar Kano ta zarce Abuja a yawan wadanda suka Kamu da cutar. Sama da mutum 300 ne ke kwance a na duba zuwa ranar Juma’a.
Sannan kuma haka mutuwa ma, mutane sai mutuwa suka yi a kullum duk da dai ana samun wadanda suke warkewa.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce gwamnati za ta yi amfani da maganin zazzabin cizon sauro wato ‘Chloroquine’ da ‘Zithromax’ domin warkar da cutar Covid-19 a jihar.
Gwamna Bala ya ce wadannan magunguna ne ya yi amfani da su har ya warke a lokacin da ya kamu da cutar.
Mohammed ya umurci ma’aikatan kiwon lafiya dake jihar su fara amfani da wadannan magunguna domin warkar da masu fama da cutar a jihar.
Ya ce saboda ana amfani da wadannan magunguna ne ya sa har yanzu babu wanda aka rasa a jihar.
“Jikin mu ya saba da wadannan magunguna domin ko zazzabi ya kama mutum za ka iya sha domin samun sauki. Sannan a maimakon mu biye wa abin da bature ke fada na rashin maganin cutar gwara mu yi amfani da abin da muke da su kawai.
Tun da cutar Covid-19 ya bullo ma’aikatan kiwon lafiya ke ta korafi kan ingancin maganin wajen warkar da cutar a duniya.
Yayin da wasu bangarorin duniya ke cewa maganin na warkar da cutar, Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da wasu kwararrun likitoci sun ce ba su da tabbacin ko maganin na iya warkar da cutar Covid-19.
Sun ce za su gudanar da bincike a kan maganin domin yawan amfani da maganin na iya yi wa jikin mutum illa.