COVID-19: Ma’aikatan lafiya 2 da almajirai 24 sun kamu a jihar Jigawa

0

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar cewa ma’aikatan lafiya biyu da almajirai 24 sun kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Abba Zakari ya Sanar da haka a daren Juma’a.

Ya ce ma’aikatan lafiyan sun kamu da cutar ne a lokacin da suke duba mutanen dake fama da cutar a asibitin FMC a Birnin-Kudu da Rasheed Shekoni dake Dutse.

Zakari ya ce akwai alamun cewa wasu ma’aikatan lafiya za su kamu da cutar a jihar ganin cewa akwai wasu ma’aikatan lafiyan da aka yi wa gwajin cutar da sakamakon su bai fito ba tukunna.

Yadda Almajirai 24 suka kamu da Covid-19

Zakari ya ce almajirai 24 da suka kamu da cutar na daga cikin wadanda aka dawo da su daga jihar Kano.

Idan ba a manta ba a cikin wannan makon ne jihar ta sanar cewa almajirai 16 ne suka kamu da cutar a jihar.

Ya ce sun yi wa almajirai 148 gwajin cutar daga cikin 607 da aka dawo da su jihar.

Sakamakon gwajin ya nuna cewa almajirai 40 na dauke da cutar.

Zakari ya ce akwai almajirai sama da 1000 dake killace a sansanin masu butane kasa dake jihar.

Ya ce an dauki jininsu domin yi musu gwajin cutar sannan za a komar da su wajen iyayen su ne bayan an tabbatar basa dauke da cutar.

An dawo da almajiran ne daga jihohin Kaduna, Kano, Filato, Nasarawa da sauransu.

A yanzu dai mutum 85 na dauke da cutar sannan mutum biyu sun mutu a jihar.

Share.

game da Author