COVID-19: Jigawa 35, Kano 26, Bauchi 20, Abuja 15, Yanzu mutum 4399 suka kamu a Najeriya, 143 sun rasu

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 248 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Asabar.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Asabar, Jihar Legas ta samu karin mutum 81, 35-Jigawa, 26-Borno, 26-Kano, 20-Bauchi, 13-FCT, 12-Edo
10-Sokoto, 7-Zamfara, 4-Kwara, 4-Kebbi, 2-Gombe, 2-Taraba, 2-Ogun, 2-Ekiti, 1-Osun, 1-Bayelsa.

Yanzu mutum 4399 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 778 sun warke, 143 sun mutu.

Jihar Bauchi ta samu karin mutum 20 ranar Lahadi. Jihar Kano, Barno, Sokoto, da Abuja sun samu karin wadanda suka kamu da cutar da dama.

An umarci Hukumar Kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gwada tabbaci da sahihancin ruwan magungunan gargajiya da aka hada da gangaye da sayun itatuwa, wadanda ake yin maganin tari da su, domin a gani ko za su iya yin maganin Coronavirus.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya ta Kasa, Abdullahi Mashi ne ya rubuta wa Shugabar Hukumar NAFDAC Mojisola Adeyeye takardar wannan umarni tun a ranar 28 Ga Afrilu, 2020.

Najeriya ba ita ce kasa ta farko da ta nemi gwada maganin gargajiya domin magance cutar Coronavirus ba.

Cikin watan Disamba kasar Madagascar ta yi amfani da ruwan maganin da aka tace daga ganyen na’a-na’a, kuma ta tabbatar cewa ya na magani, bayan ta gwada a kan mutum biyu.

Tuni gwamnatin kasar ta bada umarnin raba maganin ga dalibai, sauran jama’a kuma aka yi musu rangwame.

Ta kuma tilasta shan maganin a kasar duk kuwa da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da ingancin maganin ba, bisa dalilin cewa har yau ba a samo maganin cutar Coronavirus ba.

Tuni kasashe da dama a nan Afrika, ciki har da Tanzania suka nuna bukatar maganin daga Madagascar domin su ma su jaraba a kasashen na su.

Share.

game da Author