Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 239 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Asabar.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Asabar, Jihar Legas ta samu karin mutum 97, 44-Bauchi, 29-Kano, 19-Katsina, 17-Borno, 7-FCT, 6-Kwara
5-Oyo, 3-Kaduna, 3-Sokoto, 2-Adamawa, 2-Kebbi, 2-Plateau, 2-Ogun, 1-Ekiti.
Yanzu mutum 4151 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 745 sun warke, 128 sun mutu.
Jihar Bauchi ta samu karin mutum 44 ranar Asabar. Jihar Kano, Barno Bauchi da Abuja sun samu karin wadanda suka kamu da cutar da dama.
An umarci Hukumar Kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gwada tabbaci da sahihancin ruwan magungunan gargajiya da aka hada da gangaye da sayun itatuwa, wadanda ake yin maganin tari da su, domin a gani ko za su iya yin maganin Coronavirus.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya ta Kasa, Abdullahi Mashi ne ya rubuta wa Shugabar Hukumar NAFDAC Mojisola Adeyeye takardar wannan umarni tun a ranar 28 Ga Afrilu, 2020.
Najeriya ba ita ce kasa ta farko da ta nemi gwada maganin gargajiya domin magance cutar Coronavirus ba.
Cikin watan Disamba kasar Madagascar ta yi amfani da ruwan maganin da aka tace daga ganyen na’a-na’a, kuma ta tabbatar cewa ya na magani, bayan ta gwada a kan mutum biyu.
Tuni gwamnatin kasar ta bada umarnin raba maganin ga dalibai, sauran jama’a kuma aka yi musu rangwame.
Ta kuma tilasta shan maganin a kasar duk kuwa da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da ingancin maganin ba, bisa dalilin cewa har yau ba a samo maganin cutar Coronavirus ba.
Tuni kasashe da dama a nan Afrika, ciki har da Tanzania suka nuna bukatar maganin daga Madagascar domin su ma su jaraba a kasashen na su.
Discussion about this post