COVID-19: Bashir Ahmad zai tallafa da takunkumin fuska 5000 a Kano

0

Maitaimaka wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kafofin yada labarai na zamani, Bashir Ahmad zai tallafa wa mutan Kano da takunkumin fuska har guda 5000.

Bashir ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa kamar yadda yayi alkawarin tallafa wa mutanen garin sa wato Kano da takunkumin fuska, yanzu sun iso kuma za a aika da su Kano domin raba wa mutane.

Bashir ya saka hotunan takunkumin fuskan a lokacin da ya ke duba su bayan an kawo masa daga wurin tela.

Bayan haka ya ce zai tallafa da man tsaftace hannu kamar haka nan ba da dadewa ba.

Masoya da abokan arziki sun yo tururuwa zuwa shafin Bashir a tiwita domin yaba wa hadimin Buhari, Bashir bisa wannan himma da yayi na tallafawa mutane mallakar takunkumin fuskar.

Jihar Kano ce ta biyu a Najeriya da annobar Coronavirus ta fi yaduwa baya ga jihar Legas.

A ranar Lahadi alkaluma daga hukumar NCDC ya nuna cewa mutum sama da 4000 sun kamu da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author