Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta Sanar cewa an sallami mutum 60 daga asibitocin kula da masu fama da cutar Covid-19 a jihar.
Ma’aikatar ta ce ta sallami wadannan mutane ne bayan sakamakon gwajin cutar da aka yi musu sau biyu ya nuna cewa ba sa dauke da cutar.
Daga cikin mutum 60 din da aka sallama akwai maza 40, mata 20.
Adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar Legas sun kai 321 a yanzu haka.
Sakamakon gwajin da NCDC ta fita ya nuna cewa mutum 1,199 ne suka kamu da cutar a jihar.
Jihar Legas ke kan gaba a Najeriya da mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar.
Jihar Kano da Babban Birnin Tarayya Abuja, ke bi mata a jere.
Daga ciki mutum 829 na kwance a asibiti, an sallami 321 sannan 31 sun mutu.
Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 170 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Talata.
Alkaluman da NCDC ta fitar, Jihar Legas ta samu karin mutum 43, 32-Kano, 14-Zamfara, 10-FCT, 9-Katsina, 7-Taraba, 6-Borno 6-Ogun, 5-Oyo, 3-Edo, 3-Kaduna, 3-Bauchi, 2-Adamawa, 2-Gombe, 1-Plateau, 1-Sokoto, 1-Kebbi.
Yanzu mutum 2950 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 481 sun warke, 98 sun mutu.
Discussion about this post