Gwamnati jihar Filato ta sanar cewa an sallami mutum 6 daga asibitin kula da masu Coronavirus a jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya Nimkong Lar ya Sanar da haka ranar Juma’a a garin Jos. Lar ya ce adadin yawan masu fama da coronavirus da aka sallama a jihar ya kai mutum 10 yanzu.
“Da farko an sallami matar da ta shigo da cutar jihar ranar 7 ga watan Mayu, an sallami wasu mutum uku ranar 13 ga watan Mayu sannan a yau Juma’a aka sake sallaman mutum shida.
Lar ya ce an yi kuskure wajen Sanar da adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a jihar.
Ya ce jihar ta samu karin mutum daya da ya kamu da cutar da haka ya kawo adadin yawan mutanen dake dauke da cutar zuwa 21 a maimakon 25 da NCDC ta Sanar ranar Juma’a.
Jihar ta kuma killace mutane 225 da take zaton sun kamu da cutar.
Bayan haka sakataren gwamnatin jihar Danladi Atu ya ce Jami’an tsaro sun kama mutane da dama dake amfani da takardan bada izinin fita na boge.
Jami’an tsaron sun kuma kama direbobin motocin haya da babura dauke da fasinjoji da aka shigo da su jihar daga wasu jihohi.
Atu ya ce mutum sama da 1000 na nan a makale a iyakan kasan dake Filato da Bauchi da dalilin dokar hana tafiye-tafiye da gwamnati ta saka.
Ya kuma ce gwamnati ta sassauta dokar zaman gida dole daga daren Alhamis zuwa daren Lahadi.
Atu ya ce duk da sassauta dokar da gwamnati ta yi mutane za su ci gaba da kiyaye dokar hana walwala daga karfe 6 na yamma zuwa 8 na safe wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka.