COVID-19: An sallami mutum 12 da suka warke a jihar Legas

0

Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Legas ta bayyana cewa an sallami mutum 12 da suka warke daga cutar Covid-19 a jihar.

ma’aikatar ta fitar da wannan sanarwa ne ranar Alhamis.

Bisa ga sanarwar mutum uku daga cikin su mata ne, daya ‘yar kasar Ukraine ce sannan da maza tara.

An sallami 6 daga asibitin Yaba, 5 daga asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas, daya daga asibitin dake Ibeju-Lekki.

An sallame su ne bayan sakamakon gwajin cutar da aka yi sau biyu ya nuna cewa ba sa dauke da cutar kwata-kwata yanzu.

A yanzu dai adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar Legas sun kai 199.

Mutum 992 ne ke dauke da cutar a jihar Legas, an sallami 199 sannan 20 sun mutum.

Idan ba a manta ba Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 206 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

A bayanan da NCDC ta fitar Jihar kano ta samu karin mutum 80, 45-Legas, 12-Gombe, 9-Bauchi, 9-Sokoto, 7-Borno, 7-Edo, 6-Rivers, 6-Ogun, 4-FCT, 4-Akwa Ibom, 4-Bayelsa, 3-Kaduna, 2-Oyo, 2-Delta, 2-Nasarawa, 1-Ondo, 1-Kebbi

Yanzu mutum 1932 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 319 sun warke, 58 sun mutu.

Duk da karin yawan mutane da ake samu dauke da cutar gwamnatin Najeriya ta sassauta dokar hana walwala a Babban birnin Tarayya, Legas da Jihar Ogun.

Mutane za su ci gaba da walwala tun daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.

Share.

game da Author