COVID-19: Am sallami mutum 8 a Adamawa

0

Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar cewa an sallami wasu mutum 8 da suka warke daga cutar coronavirus a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya Abdullahi Isa ya bayyana haka a hira da yayi da manema labarai ranar Juma’a a garin Yola.

Isa ya ce am sallami wadannan mutane ne bayan sakamakon gwajin da aka yi musu sau biyu ya nuna ba su dauke da cutar.

Ya ce adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar sun kai 13 sannan 8 na kwance a asibiti.

Isa ya yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin gujewa kamuwa da cutar musamman wajen mai da hankali ga wanke hannaye da ruwa da sabulu, amfani da takunkumin fuska da tsaftace muhalli.

Mutum 21 ne suka kamu sa cutar a jihar.

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 193 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Alhamis, Jihar Legas ta samu karin mutum 58, 46-Kano, 35-Jigawa, 12-Yobe, 9-FCT, 7-Ogun, 5-Plateau
5-Gombe, 4-Imo, 3-Edo, 3-Kwara, 3-Borno, 1-Bauchi, 1-Nasarawa, 1-Ondo.

Yanzu mutum 5162 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1180 sun warke, 167 sun mutu.

A na kuma ci gaba da samun mutane da ke warkewa daga cutar a kusan kullum a fadin kasar nan duk da mutane basu kiyaye sharuddan kauce wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author