COVID-19: Alkaluman Kaduna, Abuja da Legas ya kara lulawa sama, yanzu mutum 2388 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 220 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Asabar.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Asabar, jihar Legas ta samu karin mutum 62, 52-FCT, 31-Kaduna, 13-Sokoto, 10-Kebbi, 9-Yobe, 6-Borno
5-Edo, 5-Bauchi, 4-Gombe, 4-Enugu, 4-Oyo, 3-Zamfara, 2-Nasarawa, 2-Osun, 2-Ebonyi, 2-Kwara, 2-Kano, 2-Plateau.

Yanzu mutum 2388 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 385 sun warke, 85 sun mutu.

Abu fa sai gaba-gaba yake yi yanzu. Maimakon baya sai gaba ake samu. Baya ga yaduwa da cutar tayi zuwa kusan duka jihohin kasar a kullum karin yawan wadanda suka kamu ake samu maimakon raguwa.

A karon farko jihar Kano ta samu karin mutum biyu kacal. Abuja da jihar Legas sun samu karin mutane sama da hamsin a bisa alkaluman da hukumar NCDC ta fita ranar Asabar. Jihar Sokoto da Kebbi ba sun samu karin mutane da dama da suka kamu da cutar.

Kwamishinan Kiwon lafiyar Kaduna a ranar Asabar ta bayyana cewa sakamakon mutum 167 da aka kai gwaji hukumar NCDC ya fito. Ta ce akwai yiwuwar samun karin mutane da dama da zasu kamu da cutar bayan gwajin. Wannan adadin yana daga cikin mutum 350 da aka dibi samfarin su domin gwaji.

Jihohin Sokotoa da Kebbi ma sun samu karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a ranar Asabar.

Share.

game da Author