CORONAVIRUS: Yadda ‘yan Najeriya su ka bijire wa gargadin kaffa-kaffa da juna bayan sassauta dokar zaman gida tilas

0

‘Yan Najeriya sun yi fatali da yadda cutar Coronavirus ke kisan dubban mutane da jikkata mikyoyi a duniya, yayin da suka yi fitar farin-dango a ranar Litinin sanadiyyar sassauta dokar zaman gida dole a Abuja da Jihohin Lagos da Ogun.

Tun a waccan Litinin da ta gabata ce dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sassauta dokar daga ranar 4 Ga Afrilu zuwa 17 Ga Afrilu.

An yi sassautawar ce domin a rage wa jama’a radadin kuncin rayuwa, a kauce wa barazanar rasa aiki ga dubban jama’a da kuma sake motsa igiyar ruwan tatttalin arziki.

A lokacin da Kodimata na Shirin Kwamitin Shugaban Kasa, Sani Aliyu ke jawabi, ya ce idan aka sassauta dokar, to an haramta taron jama’ar da ta kai mutum 20 a wuri daya.

Wasu daga cikin wuraren harkokin hada-hada da jama’a su ka fi yin dandazo a ranar Litinin, su ne harabar wasu bankuna kalilan da aka bude.

Bankunan da aka bai wa umarnin su yi aiki daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana, harabobin su sun cika makil da jama’a kamar wurin kallon dambe.

‘Yan Najeriya da dama sun cika da mamakin ganin yadda mutane suka rika yin abin da Bahaushe ke cewa, “shahadar-kuda”, har su ka rika watsa bidiyon wuraren da jama’a su ka yi dafifi a shafukan Twitter.

Wasu sun rika dora laifin a kan rashin iya aikin ma’aikatan bankunan, wasu kuma na cewa matsalar ta intanet ce.

https://twitter.com/YinkaPost/status/1257266638333923328?s=19

https://twitter.com/DrOlufunmilayo/status/1257242190599856128?s=19

Wadannan Rariyar Likau da ke sama, duk shafukan Twitter ne masu dauke da bidiyon yadda jama’a su ka yi cunkoso, dafifi da gwamutsuwa da juna.

Share.

game da Author