Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta bayyana cewa ya zuwa ranar Talata, 19 Ga Mayu, wadanda suka kamu da Coronavirus a Afrika sun zarce mutum 86,000.
Idan ba a manta ba, ranar 11 Ga Maris ne WHO ta bayyana cewa kasashe kowace ta yi ta kan ta, domin cutar Coronavirus ta zama mummunar annoba.
A wancan lokacin wadanda cutar ta kama a duniya ba su kai mutum 10,000.
Amma ya zuwa yanzu cutar ta kama sama da mutum milyan 4.5 a duniya, kuma ta kashe sama da mutum 300,000.
Kwanan baya WHO ta ce idan ba a dauki mataki ba, cutar za ta iya kama mutum milyan 250 a Afrika.
Safiyar Talatar nan WHO ta nuna fargabar cewa cutar za ta sake mamaye duniya fiye da halin da ake ciki a yanzu idan kasashe suka ci gaba da gaggawar janye dokar zaman gida dole da ta tafiye-tafiye, ba tare da sun yi kwakkwaran daukar matakai ba.
A bangaren Afrika, WHO ta bayyana jerin kasashen da aka fi kamuwa da cutar Coronavirus kamar haka:
Afrika ta Kudu: 16,432
Aljeriya: 7,201
Najeriya: 6,175
Ghana: 5,735
Kamaru: 3,529
Kasashen Losotho, Tsibirin Comoros da Tsibirin Seychelles ne kasashen da ke da karancin wadanda suka kamu da cutar.
Losotho: 1
Comoros: 11
Seychelles: 11.