Akalla Amurkawa milyan 1.8 ne suka daina kallon tashoshin talbijin wadanda sai an biya kudi ake kallon su.
Tashoshin satellite na Amurka sun koka cewa sun samu raguwar masu biyan kudi (subscription) su na kallon tashoshin talbijin. Wannan matsala suka ce ta faru tun daga farkon Janairu har zuwa karshen Afrilu.
Sun ce hakan ya faru ne saboda kuncin rayuwa da kasar ta fuskanta dalilin barkewar annobar Coronavirus.
Har yanzu akasarin jihohin Amurka ba a cire dokar zaman gida dole ba, wadda aka kakaba saboda barkewar Coronavirus.
Sama da mutum milyan 1,300,000 ne suka kamu da Coronavirus a Amurka, yayin da sama da mutum 280,000 suka mutu.
Ana hasashen cewa yawan wadanda za su kara daina kallon tazhoshin talbijin din za su karu matuka, saboda har yanzu harkokin hada-hadar samun kudi ba su bude ba tukunna.
Dalilai 5 Da Amurkawa Kusan Milyan 2 Suka Daina Kallon Talbijin
1. Tsadar rayuwa da kuma tsadar katin biyan kudin kallon tashoshi.
2. Mummunan kisan da cutar Coronavirus ke yi wa jama’a da kuma yawan wadanda ta kama a kasar. Wannan ya sa wasu gidajen masu kallon sun mutu, wasu kuma rashin lafiya na damun su. Don haka biyan kudin kallon tashoshin talbijin ba shi ne matsalar da ta zame musu tilas su kawar ba.
3. Dakatar da wasannin da ake kallo kai-tsaye (live). Wannan ma ya sa dimbin mutanen Amurka daina kallon tashoshin da ake zare kudi ana biya kafin a kalla.
4. Rashin Aikin Yi: Annobar Coronavirus ta sa an samu marasa aiki har kashi 15 cikin 100, kamar yadda Kamfanin Bincike na Wall Street, mai suna MoffenttNathanson ya fitar, a ta bakin shugaban su, Craig Maffett.
Sai dai kuma tashoshin talbijin irin su Hulu+ Live ta samu karin masu kallo 100,000, GoogleYouTube karin mutum 300,000 da kuma Tashar Disney + wadda ya a yanzu ta na da masu biya su na kallo a duniya sama da mutum milyan 54.5.