Cutar Coronavirus ta karade duk kasashen Afrika bayan samun kasa ta karshe da ba a samu bullar cutar ba ta bayyana.
Dama kasar Lesotho ce ta rage ba a samu labarin bayyanar cutar a can ba tun da lcutar ta diro Afrika.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lesotho ta bayyana dirar cutar a kasar ranar Laraba a lokacin da take fadin sakamakon gwajin da aka yi wa wasu matafiya 81 da suka dawo daga kasashen Afrika Ta Kudu da Saudiya.
“A ranar 9 ga watan Mayu 2020 ma’aikatar kiwon lafiya ta yi wa wasu matafiya da suka dawo kasar nan daga kasashen Afrika ta Kudu da Saudiyya, mutum 81 gwajin cutar. Sakamakon gwajin ya fito ranar 12 ga watan Mayu inda mutum daya daga cikin 81 aka samu na dauke da cutar.
“Bincike ya nuna cewa mutum daya din da ya kamu da cutar daga kasar Afrika ta Kudu ya dawo.
Jaridar ‘Africanews’ ya ruwaito cewa an yi wa mutum 597 gwajin cutar a kasar Lesotho. Sakamakon gwajin mutum 295 ya fito, ana jiran sauran na mutum 301.
A kasar Algeria kuma, gwamnatin kasar ta kafa kamfanin yin na’uran gwajin cutar a garin Algeirs.
Shugaban sashen sarrafa magunguna na kasar, Lotfi Benbahmed ya ce wannan na’ura da kasar ke yi na iya yin gwaji ya bada sakamako cinkin minti 15, kuma za a iya auna jinin mutum sama da 200 a cikin mako daya.
Benbahmed ya ce kamfanonin kasashen Jordan da Canada ne suka hada hannu da na kasar domin yin wadannan na’urorin gwaji.
Ya ce gwamnati ta ware dala miliyan 100 domin shigo da magunguna da kayan aiki domin dakile yaduwar cutar. Kuma Chana ta tallafa mata da magunguna da wasu kayan aikin.
Cutar Covid-19 ta bayyana a kasar Algeria a ranar 17 Fabrairu a jikin wani matafiyi da ya shigo kasar daga kasar Italiya.
Mutum 6,253 ne suka kamu da cutar, 522 Sun mutu sannan 3,058 sun warke.