Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya bayyana cewa akalla Jami’an Kula da Lafiya 14 ne suka kamu da cutar Coronavirus a jihar.
Masari ya yi karin bayanin cewa 10 daga cikin su duk ma’aikatan Asibitin Gwamnatin Tarayya ne da ke Katsina (FMCK), 6 kuma daga asibitoci masu zaman kan su.
Ya ce mutum 75 da suka kamu da cutar a jihar, 37 da suka kamu a baya-bayan nan daya daga Daura ya kamu da ciwon, sauran kuma a Katsina.
Da ya ke karin hasken dalilin killace Fadar Sarkin Daura, Gwamna Masari ya ce an garkame ta ne saboda jama’a sun ki bin umarnin hana gwamutsuwa wuri daya, inda dubban jama’a suka yi cincirindo a fadar, domin karbar kayan tallafi.
Ya ce Gwamnati ta yanke shawarar kara kulle garuruwan Katsina da Daura saboda jama’a har yanzu ba su nabba’a sun kiyaye bin dokoki da sharuddan yin cinkoso, cincirindo da gwamutsuwa a wuri daya ba.
Daga nan ya ce za a kara yawan wurare, shaguna da kantinan da jama’a za su rika zuwa su na sayen kayan abinci a lokacin wannan ci gaba da zaman gida dole da suka janyo aka kara kakaba musu.
Masari ya ce kuma za a karo tulin kayan kariya da jami’an kiwon lafiya ke amfani da su domin kauce wa daukar cutar Coronavirus.
A karshe ya yi kira ga jama’a da su rika zuwa su na kai kan su ana auna su.