CORONAVIRUS: Mutum biyu sun rasu a Kaduna

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu dake fama da cutar coronavirus a Jihar Kaduna sun rasu.

El-Rufai ya rubuta haka a shafin sa ta tiwita ranar Asabar.

Ya ce wadanda suka rasu din, wani dattijo ne a karamar hukumar Makarfi da wata mata a Zariya kuma an samu karin mutum biyu da suka kamu da cutar a Kaduna a ranar Asabar.

Yanzu mutum 87 suka kamu a jihar Kaduna.

kakakin gwamnatin Jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye, ya ce da yawa daga cikin wadanda suka kamu da cutar a Kaduna sannan suke yadawa matafiya ne da ke karya dokar shige da fice daga wasu jihohin kasar nan.

Mahukuntan FCTA da gwamnati ta kafa domin tilasta mutane su kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka a Abuja ta kama matafiya 43.

Shugaban kungiyar Ikharo Attah ya Sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.

Attah ya ce sun kama wadannan mutane ne tun a ranar Talata a shataletalen AYA dake Asokoro.

Ya ce wasu daga cikin su sun taso daga Abuja zuwa Kaduna, Kano da Niger.

“Wata mata da muka kama da ‘ya’yan ta biyu ta shigo Abuja daga jihar Benuwai ne.

“Duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya saka dokar hana walwala mutane da dama na karya dokar.

Attah ya ce sun hada da direbobin da fasinjoji duka, kuma za su fuskanci hukuma.

Share.

game da Author