CORONAVIRUS: Mutum 190,000 za su iya mituwa a Afrika, idan ba a tashi tsaye ba -WHO

0

Wani kwakwaran nazari da bincike da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gudanar, ya nuna cewa idan har aka yi sakaci aka kasa shawo kan annonar Coronavirus a Afrika, to cutar za ta iya kashe mutum 190,000.

Duk da cewa har yanzu yawan mace-mace sanadiyyar Coronavirus a Afrika, ko kusa bai kai nai kasashen Turai da Amurka ba, binciken ya nuna cutar za ta iya kashe mutum 82,000 zuwa 190,000, sannan kuma mutum milyan 44 za su iya kamuwa da cutar a cikin shekarar nan daya, idan ba a tashi tsaye ba.

Ya zuwa yanzu dai mutum 2127 ne suka mutu a Afrika, inda a Masar ne aka fi mutuwa, har mutum 495, Aljeriya mutum 490, Morocco mutum 183, Najeriya kuwa sama da mutum 100.

Amma kuma rahoton ya ce karancin wadanda ke mutuwa a yanzu din zai iya karuwa nunkin-ba-nunkin nan gaba, idan shirin yaki da cutar ya shiririce a Afrika.

Binciken ya nuna cewa ba a samun yawan matasa na kamuwa a Afrika da kuma yara kanana, saboda yawan amfani da magungunan da masu fama da cutar kanjamau da tarin TB suke amfani da shi wajen kara wa garkuwar jiki karfi.

“Amma ci gaba da fantsamar cutar zuwa tsawon wasu ‘yan shekaru, to zai iya ragargaza nahiyar Afrika.” Inji Daraktar WHO mai kula da Nahiyar Afrika, Matshidiso Moefi.

Moefi ta ce idan ana ganin Coronavirus ba ta yawan fantsama da sauri a yanzu kamar Turai da Amurka, to nan gaba za ta yi fantsamar da za a shafe shekara da shekaru ta na kisa da kassara jama’a a Afrika.

Ta ce mafita a yanzu shi ne kasashen Afrika su tashi su kara inganta harkokin kula da lafiya a kananan asibitocin garuruwa, kauyuka da karkara.

An tattara wannan bincike ne a kasashe 47 wadanda aka yi nazarin halin da suke ciki da al’umma akalla bilyan daya da ke cikin kasashen.

Bayanin ya na cikin Mujallar ‘Medical Journal Global Health.

Share.

game da Author