CORONAVIRUS: Mun kasa gudanar da aikin da muka je yi a Jihar Kogi -Ministan Lafiya

0

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa kokarin da kwamitin Shugaban Kasa ya yi wajen kai daukin taimaka wa Jihar Kogi wajen gano masu cutar Coronavirus ya ci tura. Haka ya bayyana a ranar Juma’a.

Da ya ke bayani a wurin taron manema labarai na yau da kullum, ministan ya ce tawagar da su ka tura Kogi ta je salum, kuma ta dawo alum ba tare da gudanar da ko daya daga aikin da ta je Jihar domin aiwatarwa ba.

“Mun tura jami’ai daga Ma’aikatar Lafiya da Hukumar NCDC zuwa Jihar Kogi, amma an samu matsala da sabanin da su ka sa tilas su ka dawo.

“Nan gaba za a sake tura wata tawaga bayan an samu daidaito da gwamnan jihar”

Tuni dai Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ke kartar kasa cewa babu wani mai dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Duk kokarin da Hukumar NCDC ta yi domin a shawo kan sa a yi wa jama’a gwaji a jihar ya ci tura.

Cikin ranar Juma’a an tura tawaga domin ta taya jihar aikin gwajin masu cutar Coronavirus, amma Gwamna Bello ya bada umarnin cewa sai an fara killace su tsawon kwanaki 14 tukunna.

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar ta gwamnatin tarayya tserowa su ka yi a guje daga Lokoja zuwa Abuja, gudun kada a yi ram da su a garkame cibiyar killace masu cutar Coronavirus.

Sai dai kuma Kungiyar Likitocin Jihar Kogi ta nuna matukar damuwa dangane da yadda duk da rashin lafiyar da ake fama da ita, amma Gwamna Bello ya ce babu wani mai cutar, kuma ba a yin gwaji a jihar Kogi.

Jihar Kogi na makwautaka da jihohin da cutar Coronavirus ta fantsama, musamman babban birnin tarayya, Abuja.

Daraktan Hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu ya nuna damuwa sosai dangane da halayyar jihar Kogi, wadda ya ce ta nuna ba ta bukatar taimakon jami’an hukumar sa.

Ya ce dama kowace jiha ita ce ke da alhakin kula da al’ummar cikin ta. Su na so kasai agaji ne.

Idan ba a manta ba, Yahaya Bello ya yi zargin cewa akwai wani jami’in da ke so a kamfaci wani adadin mutane a yi karyar cewa wai su na dauke da cutar Coronavirus a jihar, harkallar da ya ce shi ba zai taba yiwuwa ba.

Share.

game da Author