CORONAVIRUS: Matawalle ya garkame Zamfara na sati daya

0

Domin dakile yaduwar cutar coronavirus gwamnatin Zamfara ta dakatar da zuwa malallatai da coci-coci da sannan ta garkame kasuwannin jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ya Sanar da haka a daren ranar Litini. Yace wannan doka zai fara aiki ne daga ranar Litinin.

Bayan haka kuma gwamna Matawalle ya ce kamar yadda gwamnatin tarayya ta saka dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe, a jihar ma haka za ayi.

Yace dokar hana fita a karamar hukumar Kauran Namoda yanzu zai far ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Ya yi kira da a ci gaba da addu’a kan yadda mutane ke ta mutuwa a Karamar hukumar Kauran Namoda da mutuwar ta ratsa har fadar sarkin Kauran Namoda.

Gwamna ya ce gwamnati ta yi feshin fadar sarkin sannan gaba daya sannan gwamnati ta hori mutane da su bi dokar gwamnati.

A karshe Matawalle ya ce wannan abu da ke faruwa musamman a Kauran Namoda, na bukatar mutane su koma ga Allah a ci gaba da addu’a domin Allah ya kawo karshen wannan ibtila’i da ya afko.

Dokar hana walwala bai shafi kantinan saida kayan masarufi ba, abinci da magani. Sannan ya roki mutane su rika yin salloli a gidajen su saboda halin da ake ciki.

Share.

game da Author