Wani rahoto da aka wallafa a ranar Litinin ya yi nuni da cewa manoma a Afrika ta Yamma sun yi wa cutar Coronavirus fahimta daban-daban. Yayin da wasu suka yarda akwai cutar, wasu kuma sun jajirce cewa gwamnati ce kawai ta kirkiro ‘cutar Coronavirus’ don amfanin kan su da aljifan su kawai.
Sai dai kuma dukkan su sun amince cewa irin yadda gwamnatocin kasashe suka dauki matakan abin da suka kira dakile cuta, to ya gurgunta harkokin noma kwarai ainun.
Cibiyar Binciken Irin Shuka mai suna ICRISAT, wanda ke binciken irin shukar kayan noma a kasashe masu tsandaurin kasar noma a Afrika ne ta fitar da shi.
ICRISAT kungiyar kasa-da-kasa ce mai binciken harkokin bunkasa noma a yankunan karkara.
“A yanzu dai abin da ya fi bai wa manoman wannan yanki damuwa sosai, shi ne shin ko za su bazama su tafi gonakin su, idan an yi ruwan shuka. Saboda akwai bukatar a kara wayar musu da kai sosai dangane da halin da ake ciki da abin da ya kamata su rika yi. Su kuma wadanda ke da sukunin iya amfani da soshiyal midiya a cikin su, sun rigaya sun yi wa abin mummunar fahimta.” Inji rahoton.
“Mu dai sai mu ka kirkiro shirin wayar da kan manoman mu, saboda mun fahimci cewa ba a sanar da su takamaimen yadda za su rika kare kan su ba.” Inji Aichatou Nasser Salifou ta gonar Ainoma Seed Farm, a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar Shirin Samar da Abinci ta Duniya (WFP), ta ce akalla mutum milyan 40 za su fuskanci matsalar karancin abinci a Afrika ta Yamma, nan da watanni masu zuwa, dalilin annobar Coronavirus.
Wannan dalilin ne ya WFP ta ce ko shakka babu zai iya sanya dimbin jama’a ka iya kamuwa da cutar ba da dadewa ba.
Sannan kuma rahoton ya nuna cewa kananan yara wadanda ba su kai shekaru biyar ba kusan milyan 12 ne za su fuskanci karancin abinci mai gina jiki, dada watan Yuni din nan mai kamawa zuwa Agusta.
Manoman Da Suka Fi Jin Jiki A Lokacin Coronavirus:
Rahoton ya nuna cewa kungiyoyin manoma masu dimbin yawa ne su ka fi jin jiki da tafka asara sosai. Saboda su ne su ka karbi ramcen kudade da irin shukawa, amma kuma shukar da noman sun gagara.
Haka duk wasu masu zuba kudade ko jarin su da masu ruwa da tsaki a harkar noma a Afrika ta Yamma, su na kukan cewa su ma abin ya jijjiga su sosai.
“Mun ramci kudi mun yi noman iri. To saboda dokar zaman gida dole, ba mu iya fita kasuwa mu sayar da irin na mu Ga manoma. Sannan kuma akwai matsalar dokar hana cakuduwa ko gwamutsuwa a wuri daya. Saboda ba za su dauki ma’aikata da yawa su yi mana aikin zuba taki a gonaki ba. Ga kuma damina ta gabato.”
Abdul Razak da ke da gonar Kamfanin Heritage Seed Company a Ghana ne ya yi wancan kuka a sama.
A kasashe irin su Mali da sauran su, tun bayan kafa dokar hana tafiye-tafiye, an hana cin kasuwannin kauyuka ballantana kananan manoma su sayar ko su sayo. Hatta maganin kashe kwarin da ke cinye shuka ma duk manoma ba su iya samu.
“Mu yanzu wani babban abin da mu ke fuskanta shi ne matsalar jigilar kayan gona. Yanzu haka kafin ka kai kayan gona Ibadan daga Kano, sai ka shafe kusan mako biyu, saboda babu masu aikin, an kulle kowa a gida. Shi ya sa mu ke kokarin ganin an kirkiro injinan da za su rika yin wasu ayyukan da karti majiya karfi kan yi.” Inji Stella Thomas, ta Techni Seed Limited da ke nan Najeriya.