CORONAVIRUS: Legas 111, Kano 4, Kaduna 6, Saura kiris Najeriya ta zarce 9000

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 182 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 111, FCT-16, Akwa Ibom-10, Oyo-8
Kaduna-6, Delta-6, Rivers-5, Ogun-4, Ebonyi-4, Kano-3, Plateau-2, Gombe-2, Kebbi-1, Kwara-2, Bauchi-1, Borno-1.

Yanzu mutum 8915 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2592 sun warke, 259 sun mutu.

Ministan Lafiya na Najeriya ya bayyana cewa gwamnati na duba yiwuwar amfani da dakunan kwanan dalibai na makarantun gwamnati domin maida su wuraren killace wadanda suka kamu da Korona a Najeriya.

Minista Ehinare Osagie ya fadi haka a taron kwamitin Shugaban kasa kan dakile yaduwar annobar Korona a Abuja ranar Alhamis.

Ehinare ya ce Najeriya na da wuraren killace marasa lafiya 122 a jihohi 35 harda Abuja, da gadaje akalla 5000.

Ana amfani da Otel da a Legas da Abuja domin killace wadanda suka dawo daga kasashen waje.

Ana shi jawabin shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu, ya koka kan karancin wuraren killace mutane da gadajen asibiti da kasa Najeriya ke fama da su.

Ya ce tuni har sun fara duba yiwuwar killace mutane a gidajen su dakuma sallamar mutane tun ba su warke ta-tas.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 389 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Laraba.

Share.

game da Author