Shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar COVID-19 kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya gargadi mutane su daina amfani da maganin hydroxychloroquine domin warkar da cutar COVID-19.
Mustapha ya yi wannan kira ne a zaman da kwamitin ta yi a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce har yanzu masana kimiyyar Magunguna ba su tabbatar wa gwamnatin Najeriya ko maganin chloroquine na da ingancin warkar da cutar Covid-19 ba.
“Muna shaidawa wa mutane cewa har yanzu babu maganin cutar Covid-19 sannan gwamnati Najeriya ba ta samu tabbacin ko maganin chloroquine na da ingancin warkar da Covid-19 ba.
“Muna kira ga mutane da su guji shan maganin ba tare da izinin likita ba domin yana cutar da kiwon lafiyar mutane.
“Idan mutum ya kamu da cutar Covid-19 ya gaggauta zuwa asibiti.
Covid-19 a Najeriya
Akalla mutum 40,043 ne aka yi wa gwajin cutar tun bayan bullowar cutar a watan Fabrairu.
Sakamakon gwajin ya nuna cewa mutum 7,016 sun kamu da cutar a jihohin 34 a kasar nan.
A yanzu mutum 1907 sun warke, 211 sun mutu a Najeriya.
Jihar Legas na da mutum 3,093, Kano – 875, FCT – 446, Katsina – 303, Bauchi – 228, Barno – 227, Jigawa – 225, Ogun – 183, Oyo – 190, Kaduna – 170, Gombe – 144, Edo – 144, Sokoto – 113, Ribas – 80, Zamfara – 76, Kwara – 66, Filato – 70, Osun – 42, Nasarawa – 38, Yobe – 45, Kebbi – 32, Delta – 31, Adamawa – 27, Niger – 22, Ondo – 22, Ekiti – 20, Akwa Ibom – 18, Taraba – 18, Enugu – 16, Ebonyi – 13, Imo – 7, Bayelsa – 7, Abia – 7, Benue – 5, da Anambra – 5.
Matakan hana tafiya daga wannan jihar zuwa wancan jihar, hana taruka mutane da saka dokar hana walwala na daga cikin matakan hana yaduwar cutar da gwamnati ta dauka a Najeriya.