CORONAVIRUS: Kaduna ta samu mutum na farko da ya rasu a dalilin cutar

0

Wani mutum dake fama da cutar coronavirus a Kaduna ya rasu, inji kwamishinan Lafiya, Amina Baloni.

Amina tace wannan wannan mara lafiya ya rasu ne bayan fama da yayi da ciwon katsewar numfashi da mura Mai zafi.

Ya rasu tun kafin Sakamakon gwajin jininsa ya fito, da yanuna yana dauke da cutar.

Tuni dai an bizne shi kamar yadda hukumar NCDC ta gindaya.

Sannan kuma har an Yi feshin asibiti biyu da ya Kai kansa.

Kwamishinan Baloni ta yi kira ga mutane da su rika killace kansu da kuma sanar da hukuma idan suka yi mu’amula da wanda ya kamu da cutar maimakon su yada wa wasu da basu ji ba su gani ba.

Alkaluma sun nuna cewa yanzu mutum 28 ne suka kamu da cutar a jihar Kaduna, sannan akai wasu 350 da aka aika da jinin su gwaji.

” Yanzu an kammala gwajin almajirai 167 da suka dawo daga Kano. Akwai yiwuwar za a samu Karin wadanda suka kamu da cutar a kwanakin an.

A karshe ta hori mutanen jihar da su rika bin dokokin da aka saka na kiyaye cudanya da mutane da kuma saka takunkumin fuska idan za a fita.

Alkaluma daga NCDC sun nuna cewa akwai akalla mutum sama da 2000 da suka kamu da Coronavirus a Najeriya. Sama da 300 sun warke.

Jihohin Legas da Kano be suka fi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author