CORONAVIRUS: Ka sayar da jiragen Shugaban Kasa, ka rage kashe kudaden cin abincin alatu -Nasihar Atiku ga Buhari

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi la’akari da halin da kasar nan ce ciki, ya zabtare wasu kashe-kashen kudade, domin a kara samun kudin shiga, saboda yadda tattalin arzikin kasar nan ya rufta cikin wani mawuyacin hali, saboda annobar Coronavirus a duniya.

A cikin wani bayani da ya fitar a shafin sa na Facebook, Atiku ya na hankalin Buhari da ya datse yawan kasafin da suka hada da:

Kasafin 2020, wanda Atiku ya ce ya yi mamakin duk da irin faduwar darajar danyen man fetur, amma Buhari naira bilyan 72 kadai ya datse daga cikin kasafin 2020.

Na biyu shi ne yawan makudan kudaden da ake kashewa a Fadar Shugaba Buhari sa sunan kudaden cin abinci.

Atiku ya ce a wannan mawuyacin hali, kamata ya yi shugaba Buhari ya rage dabdala da shagalin walimar cin abinci.

Ya ce talakawa na cikin halin kuncin rayuwa, bai dace a wannan lokaci fadar Shugaban Kasa ta koma fadar cin kayan abincin alatu ba.

Atiku ya bukaci Buhari ya sayar da bargar jiragen Fadar Shugaban Kasa, akalla ya sayar da 8 daga cikin su, domin yin hakan zai samar da kudin shiga.

Haka kuma Atiku ya nemi kada a kashe Naira bilyan 27 wajen yi wa bangaren Majalisar Tarayya kwaskwarima. Ya ce hakan bai dace ba a wannan halin da ake ciki.

Idan ba a manta ba, lokacin da Buhari ke kamfen kafin ya hau mulki cikin 2015, ya yi alkawarin cewa idan ya hau mulki zai sayar da jiragen, amma shekaru biyar ke nan bai yi hakan ba.

Share.

game da Author