CORONAVIRUS: INEC ta ce ba za ta dage zaben gwamnan Edo da na Ondo ba

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dalilan ta na ayyana cewa duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita a kasar nan, ba zai sa ta dage zaben gwamna ba, a jihohin Edo d Ondo.

Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya shaida wa gidan talbijin na ARISE TV cewa, INEC ba za ta dage zaben jihohin biyu ba, saboda idan ta yi haka, to nan gaba kuma za ta iya rasa wani lokaci da wata ranar da za ta shirya zaben.

Cikin watan Fabrairu ne INEC ta aza ranar 19 Ga Satumba za ta yi zaben gwamnan Edo, yayin da na gwamnan Ondo kuma a ranar 10 Ga Oktoba.

Barkewar cutar Coronavirus a Najeriya ya tilasta INEC dage zaben cike-gurabu a jihohin Bayelsa, Filato da Imo.

Ganin yadda Coronavirus ke ci gaba da fantsama a Najeriya, an rika nuna damuwar ko zai yiwu kuwa a gudanar da zabukan gwamnonin ko kuma a dage zaben.

Sai dai Kakakin INEC, Okoye, ya ce, “Dokar Najeriya ta ce a tabbatar an gudanar da zaben Gwamna daga kwanaki 150 kafin wa’adin wanda ke kai ya cika, zuwa kwanaki 30 kafin wa’adin na sa ya cika.”

Okoye ya amince da cewa Coronavirus ta kawo cikas sosai a kasar nan. To sai dai ya ce abin la’akari shi ne, an rantsar da gwamnan Edo a ranar 11 Ga Nuwamba, kuma tilas a sake rantsar da sabon kafin ranar 13 Ga Octoba. Shi kuma na Ondo a rantsar da shi kafin ranar 25 Ga Janairu.

A karshe ya nuna damuwar yadda watakila Coronavirus ba za ta bar wasu samun damar yin zabe ba. To amma ya ce INEC ta na amfani ne da abin da dokar kasa ta rattaba.

Share.

game da Author