CORONAVIRUS: Gwamnatin Kano ta maida gine-ginen ta cibiyiyon killace mutane

0

Gwamnatin Jihar Kano tashi gadan-gadan ta na maida wasu gine-ginen ma’aikatunta da na hokumomi zuwa cibiyoyin killace masu cutar Coronavirus.

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasiru Gawuna ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, lokacin da ya ziyarci wuraren.

Wuraren da aka maida cibiyoyin killace masu Coronavirus din sun hada da Asibitin Abubakar Imam, Dakin Karatu na Murtala Mohammed, Cibiyar Bunkasa Yawon Bude-ido, Cibiyar Wasanni ta Karfi da kuma Otal din Daula sai kuma Asibitin Sojoji da ke kan titin filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Gwamnatin ta ce duk da ta na da wuraren killace jama’a uku a Filin Wasa na Sani Abacha, Asibitin Kwanar Dawaki da kuma Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari, to akwai matukar bukatar karin cibiyoyin killace mutane, saboda ana hasashen akwai yiwuwar samun wadanda suka kamu da cutar birjik kamar farin-dango.

Gawuna ya ce jihar ta dauki wannan mataki ne domin dakile fantsamar cutar.

“Za a fara killace mutane a otal din Daula inda aka kebe gadaje 50 a ranar Asabar. Sai kuma Asibitin Imam a ranar Litinin.”

Ana sa ran Dakin Karatu na Murtala zai dauki gadaje 200, shi kuwa Cibiyar Wasanni ta Karfi za ta dauki gadaje 300.

Hukumar NCDC a ranar Alhamis ta bayyana karuwar mutum 80 masu dauke da cutar Coronavirus.

Share.

game da Author