CORONAVIRUS: Gwamnatin Bauchi ta amince a bude masallatai da Coci-Coci

0

Gwamnatin jihar Bauchi ta janye dokar hana zuwa wuraren ibada da ta saka a jihar domin dakile yaduwar cutar Covid-19.

Gwamnan jihar Bala Mohammed ya bayyana haka ranar Laraba a zaman da ya yi da malaman addini sarakunan da kungiyoyin matasa na jihar.

Ya ce daga ranar Alhamis 21 ga watan Mayu mutane za su rika fita domin ci gaba da harkokin su a fadin jihar.

Gwamnati ta dauki wannan matakin ne bisa ga kalaman Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO cewa akwai yiwuwar za a ci gaba da rayuwa ne da wannan cuta da kumganin yadda wasu jihohi suka janye dokar hana zuwa wuraren ibada.

Haka kuma gwamna Bala ya ce jihar ta samu nasarar rage yaduwar cutar a jihar. ” Mutum 225 ne suka kamu da cutar a jihar daga ciki an sallami mutum 127, 93 na kwance a asibiti biyar sun rasu.

Mohammed ya ce za a bude masallatai da coci-Coci a jihar amma fa da sharadin cewa malaman addini za su matsa kaimi wajen ganin mabiyan su na bin dokokin da aka gindaya domin kare mutane daga kamuwa da yada cutar a jihar.

Ya kuma ce za a bude kasuwanin jihar idan kungiyoyin ‘yan kasuwa suka tabbatar wa gwamnati cewa mutane za su bi ak’idojin da aka saka.

“Gwamnati za ta zauna bayan makonni biyu domin sake duba yadda komai yake domin daukar wasu matakan.

Bayan haka gwamnati ta ce dokar hana walwala da gwamnati tarayya ta saka zai ta ci gaba da aiki da ya hada da tafiye-tafiye zuwa wasu jihohi.

Dokar hana achaba na nan kuma dokar hana daukar fiye da fasinjoji biyu a KEKE NAPEP na nan a fadin jihar.

Makarantun boko duk za su ci gaba da zama a rufe.

Haka kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar, Kuma sarkin Bauchi ya bayyana cewa ba za ayi bukukuwan sallah ba a bana.

Share.

game da Author