CORONAVIRUS: Gwamnati ta umarci NAFDAC ta gwada sahihancin magungunan gargajiya wajen warkar da masu cuta

0

An umarci Hukumar Kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gwada tabbaci da sahihancin ruwan magungunan gargajiya da aka hada da gangaye da sayun itatuwa, wadanda ake yin maganin tari da su, domin a gani ko za su iya yin maganin Coronavirus.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya ta Kasa, Abdullahi Mashi ne ya rubuta wa Shugabar Hukumar NAFDAC Mojisola Adeyeye takardar wannan umarni tun a ranar 28 Ga Afrilu, 2020.

Najeriya ba ita ce kasa ta farko da ta nemi gwada maganin gargajiya domin magance cutar Coronavirus ba.

Cikin watan Disamba kasar Madagascar ta yi amfani da ruwan maganin da aka tace daga ganyen na’a-na’a, kuma ta tabbatar cewa ya na magani, bayan ta gwada a kan mutum biyu.

Tuni gwamnatin kasar ta bada umarnin raba maganin ga dalibai, sauran jama’a kuma aka yi musu rangwame.

Ta kuma tilasta shan maganin a kasar duk kuwa da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da ingancin maganin ba, bisa dalilin cewa har yau ba a samo maganin cutar Coronavirus ba.

Tuni kasashe da dama a nan Afrika, ciki har da Tanzania suka nuna bukatar maganin daga Madagascar domin su ma su jaraba a kasashen na su.

Sai dai kuma har yanzu Ministan Lafiya Ehinere ya ce har yau ba a gwada wani maganin gargajiya a Najeriya ba, ballantana a tabbatar da inganci ko.sahihancin aikin da zai iya yi wajen kashe cutar Coronavirus.

Ya ce duk wani magani da za a gwada, tilas sai masu bincike su yi masa binciken-kwakwaf, sun tabbatar tukunna.

Ya ce hanya daya da za a fara auna ko gwada maganin da ake tunanin za iya magance Coronavirus, ita ce a fara gwada shi kan dabbobi tukunna kafin mutane.

Sinadarin magungunan da aka ce a gwada ingancin na su, an kuma yi dacen cewa duk ana amfani da su wajen kara wa abinci armashi.

Sun hada da: Albasa, citta, tafarnuwa, kuka da tattasai dangande.

Share.

game da Author