CORONAVIRUS: Gaggawar janye dokar zaman gida zai iya sa kashi 80 bisa 100 na mutanen duniya kamuwa da cutar – WHO

0

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Ghebreyesus, ya bayyana cewa wadanda ke da kwayoyin garkuwar kare jiki daga kamuwa da cututtuka a duniya, wato ‘antigen’, ba su ma wuce kashi 20 bisa 100 na mutanen duniya ba.

A kan haka ne ya nuna fargabar cewa kasashe masu gaggawar sakin jama’a su ci gaba da gudanar da harkoki, za su iya sake fadawa cikin wata mummunar guguwar fantsamar Coronavirus.

“Bincike ya nuna akasarin wadanda ake yi wa gwajin kamuwa da cutar Coronavirus a duniya kashi 20 ko kasa da haka ne ake samun ba su dauke da cutar, saboda jikin su na da sinadarin garkuwar kariyar jiki daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa. A wasu kasashen ma masu irin wannan garkuwar jiki ba su wuce kashi 10 bisa 100 ba.

Da ya ke magana a Taron WHO na 73 da a yanzu haka kwanaki biyu kenan akna gudanar da shi ta akwatinan talbijin kai-taaye, ba tare da wakilan kasashe sun hallara wuri daya ba, Ghebreyesus ya ce akwai barazanar kasashen da ke gaggawar dage doka ba tare da daukar kwakwaran matakai ba, za su iya maida wa duniya hannun agogo baya.

Ya zuwa yau dai Coronavirus ta kashe sama da mutum 300,000 a duniya, kuma mutum sama da milyan 4.5 suka kamu da cutar.

Ya ce Coronavirus na ci gaba da fantsama a duniya kamar wutar daji. Kuma babu kasar da ba ta kutsa ba.

“A halin yanzu akwai kwararrun masana kimiyya 19 da ke aiki ba dare ba rana domin gano maganin cutar Coronavirus gidigat.

Saboda haka ya kara da cewa, kasashe su guji gaggawar bude harkoki saboda wasu dalilai.

“WHO ta damu da yadda al’amurra suka yi tsaye cak a kasashen duniya. To amma bai kamata garin gyaran gantsarwa kuma a karya kwankwaso gaba daya ba.”

Ya ce Coronavirus ta na kawo cikas da koma baya wajen yaki da cututtuka da harkokin lafiya kamar shirin rage mace-macen kananan yara da iyayen su, cutar kanjamau, zazzabin maleriya, tarin fuka da sauran cututtuka.

Ya karkare da bada shawara cewa sai an gaggauta bada kulawa ta musamman ga gidajen rainon kananan yara marayu, sansanonin ‘yan gudun hijira da gidajen kurkuku. Yayin da ya na hankalin hamshakan kasashe su sake zage damtse, ya kuma yi kiran akwai bukatar agaza wa kasashe masu tasowa.

Share.

game da Author