Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 338 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Alhamis, Jihar Legas ta samu karin mutum 139, 28-Kano, 28-Oyo, 25-Edo, 22-Katsina, 18-Kaduna, 14-Jigawa
13-Yobe, 13-Plateau, 11-FCT, 8-Gombe, 5-Ogun, 4-Bauchi, 4-Nasarawa, 3-Delta, 2-Ondo, 1-Ribas, 1-Adamawa.
Yanzu mutum 7016 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1907 sun warke, 211 sun mutu.
Idan ba a manta ba shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da tswaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.
Discussion about this post