Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 229 da suka kamu da Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 90, Katsina-27, Imo-26, Kano-23, FCT-14, Plateau-12
Ogun-9, Delta-7, Borno-5, Rivers-5, Oyo-4, Gombe-3, Osun-2, Anambra-1, Bayelsa-1, 1-Anambra.
Yanzu mutum 8068 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2311 sun warke, 233 sun rasu.
Idan ba a manta ba a makin da jiya, Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa akwai yiwuwar za a fara sallaman wadanda suka kamu da Korona da suka fara jin sauki daga asibitocin kasar nan.
Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 a Abuja.
Ya ce gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne bisa ga sakamakon binciken da aka gabatar game da cutar dake nuna cewa za a iya sallaman wanda ke dauke da cutar daga asibiti idan ya fara jin sauki a jikinsa. Zai koma gida ya killace kan sa ma’aikata na zuwa suna duba shi suna bashi magani.
” Muna duba yiwuwar wannan abu har yanzu domin ganin ko za a yi aiki da shirin a kasar nan. Sannan muna wayar wa mutane kai game da haka saboda gujewa korafe-korafen da za su yi idan gwamnati ta amince a rika haka.