Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar Zaman Gida Dole a jihar Kano da mako biyu. Wannan amincewa ta fito daga shugaban kwamitin Dakile yaduwar cutar Korona, Boss Mustapha ranar Litini.
Dama kuma gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar da mako daya.
A wannan taron manema labarai shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.
CORONAVIRUS: Ku saurari sabbin matakai daga Buhari ranar Litini – Boss Mustapha
Wannan Sanarwa ya shafi jihar Kano da a makonni biyu da suka gabata shugaba Buhari ya saka dokar ‘Zaman Gida Dole’ a dalilin barkewar annobar korona a jihar.
Wannan doka dai ya nuna cewa jihohi da dama ba za su samu damar zuwa sallar Idi ba idan allah ya kai mu an kammala azumin watan Ramadan.
Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 338 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Lahadi.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Lahadi, Jihar Legas ta samu karin mutum 177, 64-Kano, 21-FCT, 16-Rivers, 14-Plateau, 11-Oyo, 9-Katsina
4-Jigawa, 4-Kaduna, 3-Abia, 3-Bauchi, 3-Borno, 2-Gombe, 2-Akwa Ibom, 2-Delta, 1-Ondo, 1-Kebbi, 1-Sokoto.
Yanzu mutum 5959 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1594 sun warke, 182 sun mutu.